Sunayen jihohi da 'yan takarar gwamnoni da suka yi nasarar samun tikitin APC a zaben fidda gwani

Sunayen jihohi da 'yan takarar gwamnoni da suka yi nasarar samun tikitin APC a zaben fidda gwani

Ana kammala zabukan fidda gwani na jam'iyyar APC a jihohin fadin kasar nan. A halin yanzu jihohi kadan ne ba su kammala zabukan ba yayin da sakamakon wasu jihohin ya bayyana.

Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya samu tikitin takarar gwamnan jihar domin zarcewa a karkashin jam'iyyar APC.

A yayin zaben da aka yi a filin wasa na MKO Abiola da ke Kuto a Abeokuta, Abiodun ya samu kuri'u 1,168 inda ya lallasa 'yan takara biyar.

Zaben fidda gwanin gwamnonin APC: Jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun tikitin takara
Zaben fidda gwanin gwamnonin APC: Jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun tikitin takara. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Delta - Ovie Omo-Agege, mataimakin shugaban majalisar dattawa ya samu nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Delta.

A zaben da aka yi a farfajiyar kwalejin ilimi da ke Delta, Omo-Agege ya samu kuri'u 1,190 ba tare da wani abokin hamayya ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Kano, Nasir Gawuna, ya lashe zaben fidda gwanin APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Enugu - A jihar Enugu, Uche Nnaji, wani dan kasuwa ne ya samu nasara inda yayi caraf da kuri'u 1,070 a zaben fidda gwanin da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta lura da shi.

Gombe - Muhammadu Yahaya, gwamnan jihar da ke neman zarcewa ne aka zaba a matsayin dan takarar gwamna a jam'iyyar APC.

Yahaya ya samu kuri'u 563 yayin da ya lallasa sauran abokan hamayyarsa.

Rivers - Tonye Cole, tsohon daratan Sahara Group shi ne yayi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar PAC a jihar Rivers.

Larry Ode, baturen zaben ya ce Cole ya samu kuri'u 986 inda yayi nasarar lallasa Ojukai, Sukonte, Michael, Benald da Magnus Abe.

Nasarawa - Abdullahi Sule, gwamnan jihar Nasarawa ya yi nasara bayan deliget sun ba shi kuri'u 698 inda ya lallasa Fatima Abdullahi, matar shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mamban kwamitin zaben fidda gwanin APC a Taraba

Kebbi - Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya, Nasiru Idris, ya yi nasarar zama dan takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam'iyyar APC.

Ya lallasa Yahaya Abdullahi inda ya samu kuri'u 1,055 daga cikin jimillar kuri'u 1,090 da aka jefa a zaben.

Katsina - Dikko Umaru Radda ya bayyana a matsayin dan takarar APC na kujerar gwamnan jihar Katsina.

Radda ya samu kuri'u 506 inda ya lallasa Mustapha Muhammad Inuwa mai kuri'u 442, Inuwa na biye da Abbbas Uma Masanawa wanda yasamu kuri'u 436.

Sanata Abubakar Yar'Adua ya samu kuri'u 32, Faruk Lawal Jobe ya samu kuri'u 7, Abdulkarim Dauda Daura ya samu kuri'u 7, Umar Abdullahi Tsauri Tata ya samu kuri'u 8, Mannir Yakubu ya samu kuri'u 65 sai Ahmed Dangiwa 220.

Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna a ranar Juma'a ya tabbata dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin APC.

Gawuna ya samu kuri'u 2,289 inda ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Sha'aban Sharada wanda ya samu kuri'u 30.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya samu kuri'u 733 inda ya yi nasarar zama dan takarar gwamnan jihar na APC ba tare da abokin hamayya ba.

Yobe - A yayin bayyana sakamakon zaben fidda gwani, Umar Kareto, baturen zaben fidda gwanin ya bayyana Mai Mala Buni a matsayin dan takarar gwamnan jihar a zaben 2023.

Kareto ya ce Buni ya samu kuri'u 805 a zaben da aka yi.

Legas - Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas ne yayi nasara a zaben fidda gwanin da aka yi a jihar a ranar Alhamis

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ne yayi nasarar samun tikitin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel