Kashim Shettima: Zaɓen Zulum Ya Gaje Ni Shine Abu Mafi Kyawun Abin Da Na Taɓa Yi a Rayuwata
- Tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce gabatar da Farfesa Babagana Umara Zulum a magajinsa shi ne mafi kyawun matakin da ya taba dauka
- Shettima ya bayyana hakan ne ta wata wallafa da ya yi a Facebook bayan Zulum ya lashe zaben fidda gwanin gwamnonin jam’iyyar APC wanda aka yi a Jihar Borno
- Zulum ya gaji Shettima ne a shekarar 2019, kuma ya kasance dan takara daya tal na jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi ranar Alhamis a Cibiyar Wasannin El-Kanemi da ke Maiduguri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno ya kwatanta gabatar da Farfesa Babagana Umara Zulum da ya yi a matsayin magajinsa a mafi kyawun matakin da ya taba dauka, Daily Trust ta ruwaito.
Shettima ya yi wannan furucin ne ta wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook bayan Zulum ya lashe zaben fidda gwanin gwamnonin na jam’iyyar APC wanda aka yi a Jihar Borno na zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A shekarar 2019 Zulum ya maye gurbin Shettima kuma a wannan zaben fidda gwanin na APC, Zulum ne kadai dan takarar gwamna. An yi zaben ne a Cibiyar Wasannin Elkanemi da ke Maiduguri ranar Alhamis.
Shettima ya nuna tsananin farin cikinsa
A wallafar da ya yi a Facebook, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Shettima wanda yanzu sanata ne da ke wakiltar Borno ta tsakiya, ya ce:
“A yau ni ne mutumin da ya fi kowa murna a doron kasa, saboda kamar kullum, tun bayan na bar ofis, Ubangiji ya ci gaba da wanke ni.
“A 2018, kai (Zulum) tare da wasu mutane tara ku ka yi takarar neman gwamnan Jihar Borno na zaben 2019, amma bayan ganin salon mulkinka cike da gaskiya da jajircewa yanzu babu wanda ya fito ya kara da kai. Alama ce ta dagewarka da kokarinka a shekaru uku da ka yi a mulki.
“Matakin da na dauka a 2018 na gabatar da kai a matsayin magajina shi ne mafi kyawun yanke shawarar da na taba yi. Ban yi nadama ba kuma da zan kara samun irin damar zan ci gaba da zabenka.”
Ya yi wa Zulum fatan nasara a babban zaben 2023 da ke matsowa
Ya ci gaba da cewa kasancewar Zulum ne wanda ya ci nasara a wannan babbar jam’iyyar ta su ta APC a yau ba kwatsam ya faru ba, kuma Insha Allah nasara na jiransa a zaben 2023 da za a yi.
Ya ce ya na taya Gwamna Zulum murna kuma mutanen Borno su na matukar alfahari da shi a matsayin shugabansu.
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani rhoton, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Ya ce:
"Muna kara matsowa shekarar 2023 inda za a yi babban zabe, amma a wuri na bai da wani muhimmanci. Ba na fatan neman wata kujera. Ban taba fatan zan zama gwamnan Jihar Borno ba ma kuma bana fatan sake neman wata kujerar da ta fi ta amma a matsayin na na musulmi, ina addu'ar abin da ya fi alheri."
Asali: Legit.ng