Hotuna: Zulum ya ci zaben fidda gwani, ya ki fitowa takarar VP, ya ce sake gina Borno ne a gabansa

Hotuna: Zulum ya ci zaben fidda gwani, ya ki fitowa takarar VP, ya ce sake gina Borno ne a gabansa

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na takarar gwamna a karkashin APC
  • Ya bayyana cewa, tunanin farfado da jihar Borno tare da sake gina ta ne yasa ya sake fitowa takarar gwamnan jihar
  • Ya kara da cewa, kisan da aka yi a Kala-Balge kwanan nan yana daga cikin dalilin da yasa yayi watsi da tayi takarar mataimakin shugaban kasa

Maiduguri, Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihaar Borno ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka yi a birnin Maiduguri da aka yi a yau Alhamis.

An yi zaben fidda gwanin a filin wasa na El-Kanemi da ke Maiduguri a ranar Alhamis da yamma kuma taron ya samu halartar masu ruwa da tsakin APC da suka hada da tsoffin gwamnoni Kashim Shettima, Ali Modu Sheriff da Maina Ma'aji Lawan.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani

Karamin ministan ayyukan gona, Mustapha baba Shehuri, tsoffi da mambobin majalisar dattawa da na jihar, Amabasadan Najeriya a China, Baba Ahmed Jidda da sauransu.

Uba Maigari Ahmadu, shugaban zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da majalisar jihar Borno, ya sanar da Zulum a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 1,411.

Ya yi bayanin cewa, an saka kuri'u 1,560 wadanda suka yi rijistar zaben fidda gwanin yayin da aka tantance kuri'u 1,411 kuma ba a samu kuri'un a suka lalace ba.

Hotuna: Zulum ya ci zaben fidda gwani, ya ki fitowa takarar VP, ya ce sake gina Borno ne a gabansa
Hotuna: Zulum ya ci zaben fidda gwani, ya ki fitowa takarar VP, ya ce sake gina Borno ne a gabansa. Hoto daga @GovBorno
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin Zulum, ya mika godiyarsa ga deliget tare da masu ruwa da tsaki wanda daga baya ya sanar da matsayarsa kan kiraye-kirayen da aka dinga masa na ya nemi kujerar mataimakin shugaban kasa.

Jawabin Zulum

"A kwanakin karshen mako kadai, sama da matasa 30 aka kashe a Kala-Balge. Wannan ya dace ya tunatar da mu irin matsalolinmu da kuma bukatar mu hada kanmu wurin farfadowa, daidatawa da kuma cigaban jihar Borno."

Kara karanta wannan

Rayuwata na cikin hadari a Kurkuku, Abba Kyari ya bayyanawa kotu

"A wannan lokacin, ina so in yi magana kan abu daya. Ban tuntubi kowa ba kafin in daga maganar ba saboda bana so in bada damar da za a shawo kaina ko akasin hakan."
"Kamar yadda duka kuka sani, APC za ta yi zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabancin kasa a ranakun karshen makon nan.
"Na ga dukkan ire-iren labarai a kafafen yada labarai har da takardun manyan marubuta da makusantana kan neman takara a 2023," yace.
"Bari in ba ku hakuri, wasu daga cikin manyan 'yan takarar shugabancin kasa sun bukaci in zama mataimakinsu a takararsu, amma sai an ga sakamakon zaben fidda gwani na karshen mako.
“Na yi dogon nazari akan wannan tayi saboda zama mataimakin shugaban kasa abu ne mai ban sha'awa. Na yi tunani kan dukkan ikon. Ina hango karamar da ke cikin ganawa da gwamnoni da ministoci, damar shiga jirgin shugaban kasa. Ina hango karamar hakan a ciki da wajen Najeriya."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

“Sai dai, na tambaya kaina idan na samu damar zama mataimakin shugaban kasa kuma na daga darajata, me zai faru da ayyukan da muka fara yi wa jama'ar jihar Borno?"
"Mun gina sama da gidaje N10,000 kuma yanzu muna gyara wasu tare da kokarin dawo da mutanenmu gida. Mun dawo da jama'ar yankuna sama da 20 a yanzu."
“Akwai dubban 'yan jihar nan da suke zaune babu gidaje kuma suna bukatar abinci, ruwa da kiwon lafiya," ya kara da cewa.
“Mun rungumi tsarin cigaba wanda yanzu haka muke tabbatarwa. Na tambaya kaina, me zai faru da duk wannan tsarikan da ke taimakawa wurin farfado da jihar Borno?
"Kisan da aka yi a Kala-Balge yana daga cikin abinda ya tsunduma ni a zurfin tunani kuma lamarin ya tunatar da ni kalubalen da a yanzu suke gabanmu a jihar Borno.
"Daga nan ne na yanke hukuncin cewa, idan na samu na zama mataimakin shugaban kasa, hakan zai amfane ni. Amma idan na zama gwamnan Borno, hakan zai amfani jama'ar jihar Borno ne," ya jaddada.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel