Da dumi-dumi: An bindige mamban kwamitin zaben fidda gwanin APC a Taraba

Da dumi-dumi: An bindige mamban kwamitin zaben fidda gwanin APC a Taraba

  • Labarin dake shigowa daga Jalingo na nuna cewa an kaiwa daya daga cikin mambobin kwamitin asibiti hari
  • Shugaban kwamitin yace an bindige shi kuma an garzaya da shi gadon asibiti
  • Jihar Taraba kadai ta zabi tsarin yar tinke wajen zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan APC

Jalingo - An bindige daya daga cikin mambobin kwamitin shirya zaben fiddan gwanin jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Taraba.

Yanzu haka an garzaya da shi asibiti rai hannun Allah, rahoton ChanneltsTV.

Shugaban kwamitin, Lawrence Onuchukwu, ya laburtawa manema labarai a hedkwatar hukumar yan sandan jihar dake Jalingo, da daren Alhamis.

Da dumi-dumi: An bindige mamban kwamitin zaben fidda gwanin APC a Taraba
Da dumi-dumi: An bindige mamban kwamitin zaben fidda gwanin APC a Taraba
Asali: Original

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP

A Neja kuwa, wasu ‘yan bindiga sun kashe deliget-deliget uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin zabe kuma mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Lawrence Ewhrudjakpo ne ya sanar da haka a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar, wurin da aka gudanar da zaben fidda gwanin.

An ce an kashe su ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke komawa Mariga bayan da jam’iyyar ta dage zaben fidda gwanin sakamakon zanga-zangar da wasu ‘yan takara suka yi da nuna rashin amincewa da jerin sunayen wasu deliget din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel