Sha'aban Sharada na zargin ana shirin tafka magudi a zaben fidda gwani saboda Gawuna
- Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a APC, Sha'aban Sharada, ya koka da yunkurin magudi da gwamnatin jiha ta ke yi a zaben fidda gwani
- Sharada ya zargin gwamnatin da hana wasu deliget zabe inda za su bar wasu su yi sannan su yi amfani da sakamakon saboda Gawuna yayi nasara
- Yaaike wasika ga INEC, kwamishinan 'yan sanda, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da su duba lamarin domin gudun abinda zai iya haifarwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar APC, Sha'aban Sharada, ya koka kan shirin da gwamnatin jihar ke yi na tafka magudin zaben fidda gwani saboda mataimakin gwamna Nasiru Gawuna.
Wannan korafin na dauke ne a wata takarda da aka sanya hannu a ranar Alhamis kuma aka aike ta zuwa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ta hannun hukumar INEC ta Kano.
An aika kwafin wasikar ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, sifeta janar na 'yan sanda, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano da kuma hukumar tsaro ta fararen kaya ta jihar Kano.
A wasikar, Sharada, mamba mai wakiltar mazabar Kano Municipal a majalisar wakilai, ya zargi cewa ana shirin ne domin hana wasu deliget zabe sai dai wasu kalilan wadanda za su zama a madadin sauran, Daily Nigerian ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda yace, wannan karantsaye ne ga kundin tsarin jam'iyyar APC da kuma tsarikan zaben fidda gwani.
Ya ce: "Zaben fidda gwamnin jam'iyyar PAC na shekarar 2022 na jihar Kano an tsara shi daga shugaban APc na jihar da mukarrabansa. Za a juya kwamitin zaben fidda gwanin wanda hedkwatar jam'iyyar ta kasa ta kafa domin a samu Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan jihar Kano ya samu nasara.
"Deliget da yawansu sun yi min korafi kan yadda ake gudanar da zaben kan cewa an hana dukkansu yin zabe amma za a zabi kadan daga cikinsu su yi wadanda za ayi amfani da sakamakon.
"A don haka nake roko da a duba wannan lamari domin a samu a yi zaben gaskiya da gaskiya kamar yadda kundin tsarin jam'iyyar APC ya tanadar kuma a guje wa shari'a da za ta iya fallasa muna-munar jam'iyyar da mummunan illa da rashin samar da dan takara za ta janyo a zabe mai zuwa."
Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC
A wani labari na daban, 'dan majalisar dake wakiltar mazabar Bagwai/Shanono a majalisar jiha, Ali Ibrahim Isah Shanono, ya dawo jam'iyyar APC bayan wasu kwanaki da canza sheka daga jam'iyya mai kayan marmari (NNPP).
Daily Trust ta ruwaito yadda 14 daga cikin 'yan majalisar jihar Kano suka canza sheka daga jam'iyya APC da PDP zuwa jam'iyyar NNPP.
Shima shanono, 'dan jam'iyyar APC ya canza sheka zuwa NNPP, amma daga bisani ya yi watsi da sabuwar jam'iyyar inda ya dawo jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng