Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC

Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC

  • 'Dan majalisar jihar mai wakiltar yankin Bagwai/Shanono ya sake dawowa jam'iyyar APC bayan wasu kwanaki da canza sheka zuwa jam'iyyar NNPP
  • Manema labarai sun ruwaito yadda 14 daga cikin 'yan majalisar jihar Kano suka canza sheka daga jam'iyyar APC da PDP zuwa NNPP
  • 'Dan majalisar ya dauki alkawarin daura damarar aiki tukuru don ganin jam'iyyar APC tayi nasara a zabe mai karatowa na shekarar 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - 'Dan majalisar dake wakiltar mazabar Bagwai/Shanono a majalisar jiha, Ali Ibrahim Isah Shanono, ya dawo jam'iyyar APC bayan wasu kwanaki da canza sheka daga jam'iyya mai kayan marmari (NNPP).

Daily Trust ta ruwaito yadda 14 daga cikin 'yan majalisar jihar Kano suka canza sheka daga jam'iyya APC da PDP zuwa jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran NNPP da ya bi Ganduje, ya janye jiki ya dawo Kwankwasiyya bayan awa 24

Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC
Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shima shanono, 'dan jam'iyyar APC ya canza sheka zuwa NNPP, amma daga bisani ya yi watsi da sabuwar jam'iyyar inda ya dawo jam'iyyar APC.

A wata takarda da ya tura wa majalisar, 'dan majalisar ya cire kansa daga jam'iyyar NNPP mai kayan marmari zuwa APC.

Yallabai Ishah Shanono ya dauka alkawarin aiki tukuru don ganin APC tayi nasara a zabe mai karatowa.

Lissafin siyasar Kano na zaben shekarar 2023 na canzawa.

Sanata Ibrahim Shekarau ya canza sheka daga APC zuwa NNPP a ranar Laraba.

Jiga-jigan jam'iyyar APC da dama sun canza sheka zuwa jam'iyya mai tasowa ta NNPP.

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

A wani labari na daban, jam'iyyar NNPP ta kwatanta dan takarar shugabancin kasa a karkashin ta, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin "ma'aikin Ubangiji" wanda yake son yakar yunwa da sake hada kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Shekarau ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam’iyyar NNPP

Rahoton Daily Nigerian ya ce, Rabaren Emma Agubanze, mamban kwamitin tuntuba na addini na NNPP ya sanar da hakan a Legas a ranar Laraba. Ya ce za a yi zaben 2023 lafiya kalau kuma Kwankwaso ne da jam'iyyar za su yi nasara.

"Ya kasance a rubuce, ba Kwankwaso bane kadai batun. Gaskiyar lamarin, taimakon Ubangiji ya zo Najeriya a lokacin da zaben 2023 ke gabatowa. "

Asali: Legit.ng

Online view pixel