DG: Peter Obi ba zai shiga NNPP, su yi takara tare da Kwankwaso a zaben 2023 ba

DG: Peter Obi ba zai shiga NNPP, su yi takara tare da Kwankwaso a zaben 2023 ba

  • Doyin Okupe ya yi maganar farko tun bayan da Peter Obi ya bada sanarwar ficewarsa daga PDP
  • Dr. Okupe shi ne Darekta Janar na jirgin yakin neman zaben Peter Obi a matsayin shugaban kasa
  • Hadimin tsofaffin shugaban na Najeriya ya tabbatar da Obi ba zai nemi takara a jam’iyyar NNPP ba

Abuja - Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi watau, Dr. Doyin Okupe, ya yi magana a game da jita-jitar komawarsu jam’iyyar NNPP.

Da yake zantawa da jaridar Punch a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu 2022, Doyin Okupe ya tabbatar da cewa Peter Obi ba zai sauya-sheka zuwa NNPP ba.

Tsohon hadimin shugaban Najeriyan ya ce Obi ba zai yarda ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, a kowace jam’iyyar siyasa ba.

Okupe ya nuna sam babu yiwuwar dunkulewar tsohon ‘dan takarar kujerar shugaban kasar na jam’iyyar PDP da Rabiu Kwankwaso da zai yi takara a NNPP.

Kara karanta wannan

‘Dan tsohon Gwamnan da ya rasu, Surukin Ganduje ya lashe zaben takarar ‘Dan Majalisa

“Shi (Obi) ba zai shiga jam’iyyar NNPP ba. Za ku iya cewa ni na fada maku wannan.”
“(Obi) ba zai karbi tayin zama matamakin shugaban kasa a kowace jam’iyya ba.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Dr. Doyin Okupe

Peter Obi da Kwankwaso
Peter Obi a gidan Kwankwaso kafin zaben 2019 Hoto: @saifullahiHon
Asali: Twitter

Jaridar ta rahoto Dr. Okupe yana mai cewa a safiyar ranar Laraba, tsohon gwamnan na jihar Anambra zai bada sanarwar sabuwar jam’iyyar da zai shiga.

Obi ya hadu da Kwankwaso

Kamar yadda labarin ya zo, Cif Obi ya gana da Rabiu Kwankwaso wanda yake shirin takarar shugabancin kasa a NNPP, amma ba su iya cin ma matsaya ba.

Bayan ficewar Peter Obi daga PDP da janye takararsa, rade-radi sun fara yawo cewa ‘dan siyasar zai hadu da Kwankwaso domin su gwabza da APC da PDP a 2023.

NNPP za ta ba Obi takara?

Mutane a shafin Twitter sun kawo shawarar a tsaida Obi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a NPPP, sai Sanata Kwankwaso ya yi takarar mataimakin kasa.

Kara karanta wannan

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

Sai dai kun ji hakan zai yi wahala domin tsohon gwamnan na Kano ne ya tado jam’iyyar adawar.

Zabin da Obi yake da su

Ana tunanin Peter Obi zai nemi wata jam’iyyar hamayya da zai shiga domin yin takara. Dazu kun ji labari cewa babu mamaki tsohon Gwamnan ya shiga LP.

Mu na ganin Jam’iyyar Labor Party ta fi APGA karbuwa a wajen kudu maso gabashin Najeriya. Wasu rade-radi sun nuna akwai yiwuwar hakan ta faru.

Mun yi yunkurin jin ta bakin Buba Galadima a kan wannan batu, amma ba mu same shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng