Cikakken jerin 'yan kwamitin da za su yi wa Jam’iyyar PDP aikin tsaida ‘dan takaran 2023

Cikakken jerin 'yan kwamitin da za su yi wa Jam’iyyar PDP aikin tsaida ‘dan takaran 2023

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark zai jagoranci kwamitin zaben tsaida gwani na PDP
  • David Mark zai yi aiki tare da Ifeanyi Ugwanyi da kuma Ibrahim Shema a matsayin sakatarensa
  • Gwamnonin jihohi da tsofaffin Gwamnoni za su rike shugabancin kananan kwamitocin zaben gwanin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitocin da za su shirya zaben tsaida gwani na ‘dan takarar shugaban kasa da za ayi a 28 da 29 na watan Mayun 2022.

Premium Times ta ce babban kwamitin gudanarwan zai yi aiki ne a karkashin jagorancin Sanata David Mark da kuma Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwanyi.

Tsohon gwamnan Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema shi ne zai zama sakataren kwamitin.

David Mark shi ne kuma shugaban karamin kwamitin zabe, inda a wannan kwamiti Diri Douye zai zama mai taimaka masa, sai Ibrahim Shema zai zama sakatare.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola

A karamin kwamitin kudi akwai mutane 19, Godwin Obaseki da Ahmed Makarfi su ne shugabanni. Daniel Woyengikuro aka zaba a matsayin sakatare.

Rahoton ya ce Darius Ishaku zai jagoranci mutum 23 a kwamitin ayyuka na musamman. Zai yi aiki tare da Abdulfatah Ahmed da sakatarensa, Awwal Tukur.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Gwamna Okwesilieze Nwodo zai jagoranci kwamitin lafiya tare da Sham Zagbayi. Sakataren karamin kwamitin mai mutum 83 shi ne Dan Orbih.

Jam’iyyar PDP
Atiku a wajen neman kuri'un PDP Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Gwamnonin Benuwai da Abia, Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu za su kula da kwamitin jigila da muhalli tare da Biodun Olujimi da Abdulrahman Mohammed.

Seyi Makinde da IGP Solomon Arase (rtd) aka ba nauyin kula da tsaro. Alhaji Saad da Gurama Bawa za su rike matsayin sakatorori na kwamitin mai mutane 55.

Har ila yau, Jaridar ta ce kwamitin sufuri yana karkashin Ibrahim Dankwambo da Ike Ekweremadu. Jerry Gana ne zai kula da kwamitin yada labarai.

Kara karanta wannan

Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

Emeka Ihedioha da Taofeek Arapaja za su jagoranci kwamitin bada wurin zama sai Dr. Ifeanyi Okowa da Ahmadu Fintiri za su tantance masu kada kuri’u a zaben.

Kwamitin jin dadi da walwala yana karkashin Stella Effah-Attoe yayin da sakataren PDP, Sam Anyawu zai jagoranci kwamitin sakarariya tare da wasu mutane 41.

Asali: Legit.ng

Online view pixel