Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola

Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola

  • Sanata Aishatu Binani ta zama Zakarar gwajin dafi a siyasar jihar Adamawa da ma Arewa gaba daya
  • Yar majalisar dattawar ta kayar da manyan jiga-jigan siyasa biyar a jhar dake Arewa maso gabas
  • Yanzu za ta shiga damben kuri'u da Gwamnan jihar Mai ci, Umar Ahmadu Fintiri a zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - Sanata Aishatu Binani ta lallasa gardawa biyar a zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.

Binani ta zama mace ta farko da ta lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Adamawa

Aishatu Binani wacce yanzu haka Sanata ce mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ta lallasa tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindow da tsohon Shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu.

Hakazalika cikin wadanda ta lallasa akwai dan majalisar wakilai, AbdulRazaq Namdas, Wafari Theman da Umar Mustapha.

Kara karanta wannan

APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 7 za su rasa kujerunsu a 2023

Shugaban kwamitin zaben, Gamba Lawan, yayin sanar da sakamakon ya bayyana cewa Binani ta samu kuri'u 430, inda Nuhu Ribadu ya samu 288.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola
Da duminsa: Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola Hoto: ChannesTV
Asali: Twitter

An tattaro cewa Binani ta rabawa kowani Deleget Naira milyan daya bayan kyaututtuka daban-daban da tayi.

An fara zaben ne misalin karfe 11:30 na daren Alhamis kuma aka kammala misalin karfe 8:44 na safiyar Juma'a.

Adadin kuri'un da kowani dan takara ya samu:

Sunan dan takaraAdadin kuri'unsa
Aisha Binani430
Nuhu Ribadu288
Jibrilla Bindow103
Abdulrazak Namdas94
Umar Mustapha39
Wafari Theman21

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

An damke wasu yan siyasa biyu da ake zargin masu yiwa Sanata Aisha Binani yakin neman zabe ne suna rabawa Deleget makudan kudi a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Aisha Binani, wacce Sanata ce mai wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya a yanzu tana neman zama gwamnan jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sanatar ta yiwa Deleget alkawarin basu ninkin duk kudin da sauran yan takara suka basu.

An tattaro cewa sun fara tuntubar Deleget kenan don raba musu kudi yayinda aka fara zaben fidda gwanin dake gudana da daren nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel