Kano: Dakataccen Shugaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa, Muhuyi, Ya Janye Daga Takarar Gwamna, Ya Ci Zaɓen Sanata

Kano: Dakataccen Shugaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa, Muhuyi, Ya Janye Daga Takarar Gwamna, Ya Ci Zaɓen Sanata

  • Muhuyi Magaji Rimingado, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa ta Jihar Kano ya janye daga takarar gwamna a PDP
  • Muhuyi ya ce magoya bayansa da masu ruwa da tsaki suka bashi shawara kuma ya ga cewa hakan shine mafi dacewa ga Kano da PDP
  • Bayan janyewarsa daga takarar ta gwamna, Muhuyi ya karbi tikitin takarar sanata kuma ya yi nasarar zama dan takarar sanata na PDP a Kano ta Arewa

Jihar Kano - Dakataccen shugaban hukumar karban korafe-korafe da yaki da rashawa na Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado ya janye daga takarar gwamna a Kano a inuwar jam'iyyar PDP.

Amma, ya yi nasarar zama dan takarar sanata na mazabar Kano ta Arewa a karkashin jam'iyyar na PDP kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP

Kano: Dakataccen Shugaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa, Muhuyi, Ya Janye Daga Takarar Gwamna, Ya Ci Zaɓen Sanata
Kano: Dakataccen Shugaban Hukumar Yaƙi Da Rashawa, Muhuyi Magaji Rimingado, Ya Janye Daga Takarar Gwamna, Ya Ci Zaɓen Sanata. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Magoya baya na da masu ruwa da tsaki suka bani shawarar janye wa - Muhuyi

Ya tabbatarwa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis yana cewa magoya bayansa da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar suka bashi shawarar daukan matakin, wanda ya ce ya yi imanin hakan shine mafi dacewa ga yankinsa da PDP ta Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muhuyi, wanda ake yi wa kallon yana cikin yan takarar gwamnan a PDP da ke kan gaba, ya fito ne daga bangaren PDP da ke biyayya ga tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Aminu Wali karkashin jagorancin Shugaban PDP na Arewa maso Yamma, Bello Hayatu Gwarzo.

Duk da cewa a safiyar Alhamis ba a kammala zaben fidda gwani da bangaren Gwarzo suka yi ba zuwa safiyar ranar Alhamis, Mohammed, dan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha, shine ya yi nasarar zama dan takarar gwamna na PDP a bangaren su Shehu Sagagi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel