Shehu Sani ya sha kashi a zaben ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, ya tsira da kuri’u 2
- Bisa dukkan alamu an san wanda ya lashe zaben tsaida gwanin gwamnan jihar Kaduna a PDP
- Sanata Shehu Sani ya taya Hon. Isah Ashiru Kudan murnar zama ‘dan takarar jam’iyyar adawa
- Isah Ashiru Kudan ya doke Shehu Sani wanda ya samu kuri’u biyu da wasu masu neman kujerar
Kaduna - Burin Shehu Sani na zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023 ba zai cika ba, a sakamakon rashin nasarar da ya yi a zaben fitar da gwani.
Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa Sanata Shehu Sani bai iya samun tikitin PDP ba.
‘Dan siyasar ya tabbatar da wannan a Twitter da asuban ranar Alhamis. Sani ya taya wanda ya yi nasara murna, ya yabawa wadanda suka ba shi kuri'arsu.
Tsohon Sanatan ya sha kashi a hannun Honarabul Isah Ashiru Kudan a zaben fitar da ‘dan takarar da aka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022.
Jawabin Shehu Sani
“An kammala zaben tsaida gwanin ‘dan takarar jam’iyyar PDP na jihar Kaduna. Na fadi, kuma Hon. Isah Ashiru ya yi nasara.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina mai taya sa murna. ‘Ya ‘yan jam’iyya biyu suka zabe ni, ba tare da na ba su ko kobo ba. Abin takaici, ban san wanene su ba.”
“Saboda haka ina godewa wadannan kuri’u masu tsabta. Sai mu tari gaba.” – Shehu Sani.
Sakamakon zaben PDP a Kaduna
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, Isah Ashiru Kudan ya zo na daya a wannan zabe, ya doke wasu mutum shida, har da tsohon gwamnan Kaduna.
Sakamakon zaben ya nuna Kudan ya samu kuri’u 414, tsohon shugaban hukumar NEMA ta kasa watau Sani Sidi shi ne wanda ya zo na biyu da kuri’u 260.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero ya samu kuri’a 28. ‘Ya ‘yan jam’iyya 15 su ka zabi Sani Abbas, sai mutum 11 suka kada kuri’a ga AG Haruna.
Shehu Sani da bakinsa ya shaida cewa kuri’a biyu ya samu, kuma ya na mai matukar alfahari da su.
Asali: Legit.ng