Mai neman takara da Gwamna ya amince da shan kashi kafin fara zaben gwani a PDP

Mai neman takara da Gwamna ya amince da shan kashi kafin fara zaben gwani a PDP

  • Rahotanni sun nuna Hazeem Gbolarunmi ya hakura da shiga zaben tsaida 'dan takara a jihar Oyo
  • Dr. Hazeem Gbolarunmi ya fito neman tikitin jam’iyyar PDP, ya na neman ja da Gwamna Seyi Makinde
  • A jihar Delta, ‘diyar tsohon Gwamna ta yi galaba kan Hadimin Gwamna mai-ci a takarar majalisa

Oyo - A yau Laraba ake zaben tsaida gwani na kujerar gwamna a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a jihohin da za ayi zabe a shekara mai zuwa.

Oyo ta na daya daga cikin jihohin da za a gudanar da zaben gwamna a shekarar 2023, don haka a yau za a san wanda PDP za ta tsaida ya yi takara.

Abokin hamayyar Gwamna Seyi Makinde wajen neman tikitin takarar kujerar gwamna a jam’iyyar ta PDP a jihar Oyo shi ne Hazeem Gbolarunmi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

A ranar 25 ga watan Mayu 2022, Dr. Hazeem Gbolarunmi ya shaidawa Duniya cewa ya hakura.

Hazeem Gbolarunmi ya sallama

Kamar yadda rahoton ya zo mana, tsohon mataimakin gwamnan jihar na Oyo ya yarda ya sha kashi a zaben tsaida gwanin tun kafin a shiga filin zabe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan na zuwa ne bayan Hazeem Gbolarunmi ya sha alwashin hana Seyi Makinde komawa gidan gwamnati kamar yadda aka saba gani a jihar Oyo.

'Yar takara a PDP
Erhiatake Ibori-Suenu Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

A baya, Gbolarumi ya zargi gwamnan da cin amanar wadanda suka taimaka wajen ba shi nasara, ya ce don haka dole sai a hana shi samun tikitin tazarce.

Siyasar jihar Oyo

Gwamnonin Oyo irinsu Rashidi Ladoja da Adebayo Alao-Akala ba su iya zarcewa a kan mulki ba a dalilin fadi babban zabe ko tsige su a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Shahararren gwamnan Arewa ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP

Gwamnan farko a tarihin jihar da ya yi shekara takwas a mulki shi ne Marigayi Abiola Ajimobi.

Ba kasafai aka saba ganin gwamna mai-ci ya rasa tikitin jam’iyyarsa ba, ko da hakan ya taba faruwa da Abubakar Mala Kachalla da Akinwumi Ambode.

Erhiatake Ibori-Suenu ta samu takara

A jihar Delta, labari ya zo cewa Erhiatake Ibori-Suenu, ta doke ‘Dan majalisar tarayya mai-ci, Ben Igbakpa wajen samun tikitin jam'iyyar PDP a mazabar Ethiope.

Erhiatake Ibori-Suenu wanda ta samu kuri’a 46, diya ce a wurin tsohon gwamnan Delta, James Ibori. A karshen zaben na PDP, Hon. Igbakpa ya tashi da kuri’u 22.

PDP ta shiga tsilla-tsilla a Kano

Wani rahoto da mu ka fitar ya nuna Har yanzu an gagara fahimtar su wanene za su yi wa PDP takarar kujerun majalisa a jihar Kano a dalilin rigimar cikin gida.

Bangarorin Shehu Sagagi da na Bello Gwarzo sun gudanar da mabambantan zaben tsaida gwani. Sai a ranar Alhamis kotu za ta raba gardamar rikicin shugabanci.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng