Kano: Kotu ta jaddada Shehu Sagagi, na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban PDP

Kano: Kotu ta jaddada Shehu Sagagi, na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban PDP

  • Wata kotu da ke zama a jihar Kano ta tarayya a ranar Talata ta jaddada Shehu Sagagi a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na Kano
  • Shehu Sagagi, wanda na hannun daman Kwankwaso ne, an dakatar da shi daga ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar PDP
  • Kotun ta ce Bello Bichi, wanda ya shigar da karar bashi da hurumin hakan saboda bai kasance mamba na shugabannin jam'iyyar ba

Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano a ranar Talata ta janye umarninta na hana shugaban jam'iyyar PDP, Shehu Sagagi daga bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar.

Ana zargin Sagagi na hannun dama ne ga gwamnan Kano kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

Kano: Kotu jaddada Shehu Sagagi, na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban APC
Kano: Kotu jaddada Shehu Sagagi, na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban APC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A ranar 17 ga watan Mayu, Alkali A.M Liman ya bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da shugabannin jam'iyya karkashin shugabancin Sagagi a Kano daga amfani da wani karfin iko har sai an kammala jin karar.

Bello Bichi ne ya shigar da karar hukumar zabe mai zaman kanta, PDP da wasu mutum 40.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin janye umarnin a ranar Talata, Alkali Liman ya ce mai kara, Bello Bichi, ya kautar da kotu inda ta yarda da cewa akwai bukatar gaggawa kan lamarin.

Ya kara da cewa, Bichi ba shi da karfin shigar da karar saboda bai bayyana wata shaida cewa shi mamba na kwamitin shugabannin jam'iyyar.

Alkali Liman ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Mayu.

Ana hege a Kano: Kwanaki kadan da barin APC zuwa NNPP, dan majalisa ya sake komawa APC

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

A wani labari na daban, 'dan majalisar dake wakiltar mazabar Bagwai/Shanono a majalisar jiha, Ali Ibrahim Isah Shanono, ya dawo jam'iyyar APC bayan wasu kwanaki da canza sheka daga jam'iyya mai kayan marmari (NNPP).

Daily Trust ta ruwaito yadda 14 daga cikin 'yan majalisar jihar Kano suka canza sheka daga jam'iyya APC da PDP zuwa jam'iyyar NNPP.

Shima shanono, 'dan jam'iyyar APC ya canza sheka zuwa NNPP, amma daga bisani ya yi watsi da sabuwar jam'iyyar inda ya dawo jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel