APC Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Yau Talata Yayin Da Jami'an EFCC Suka Mamaye Gidan Okorocha

APC Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Yau Talata Yayin Da Jami'an EFCC Suka Mamaye Gidan Okorocha

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki za ta fara tantance yan takarar shugaban kasar ta a ranar Talata 24 ga watan Mayun 2022, rahoton jaridar Leadership.

Sakataren shirye-shirye na jam'iyyar na kasa, Suleiman Argungu, wanda ya sanar da hakan ranar Litinin, ya ce jam'iyyar tantance yan takarar shugaban kasa, wadanda suka siya fom, a ranar Talata, 24 ga watan Mayun a otel din Transcorp a Abuja.

APC Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Ranar Talata
APC Za Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Ranar Talata. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Jam'iyyar a ranar Lahadi, ta dage tantancewar karo na biyu kuma bata bada wani takamamen dalili ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership, ta gano cewa hakan ba zai rasa nasaba da kokarin rage yawan takarar da ke neman tikitin takarar shugabancin kasar.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

Jam'iyyar ta za ta tantance yan takarar majalisun tarayya a ranar Asabar , 28 ga watan Mayun 2022 a maimakon ranar 26 ga watan Mayu tare da yan takarar gwamna.

'Yan takarar shugaban kasa da suka cika fom dinsu suka mayar

Yan takarar shugaban kasa na APC da suka cike fom dinsu suka mayar sun hada da Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Jagoran APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu; tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.

Saura sun hada Gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade; Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi; Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani.

Akwai kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; takwararsa na Jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar; tsohon gwamnan Jihar Zamfara; Ahmed Yerima; tsohon ministan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu; tsohon gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha da tsohon gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosu.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel