Wasikar Obasanjo zai taimakawa Buhari wajen samun nasara a zaben 2019

Wasikar Obasanjo zai taimakawa Buhari wajen samun nasara a zaben 2019

- Shugaban kungiyar magoya bayan Buhari ya shawarci shugaban kasa kada ya dauki Obasanjo a matsayin makiyin sa

- Ovo Ofigo ya ce Buhari yayi amfani da wasu batutwa da Obasanjo ya fada a wasikar da ya rubuta masa ya gyara siyasar sa

An shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buari kada ya dauki, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a matsayin makiyin sa saboda budadiyar wasikar da Obasanjo ya rubuta yana kalubalanatar gwamnatin sa.

An shawarci Buhari yayi amfani da wasu abubuwa da Obasanjo ya rubuta a wasikar sa wajen gyara siyasar sa dan ba makiyan sa kunya a 2019.

Shugaban kungiyar magoya bayan Buhari, Ovo Ofigo, ya bayyana haka a zantawar da yayi da ‘yan jaridar Sunday Punch a ranar Asabar.

Wasikar Obasanjo zai taimaka wa Buhari samun nasara Buhari a zaben 2019
Wasikar Obasanjo zai taimaka wa Buhari samun nasara Buhari a zaben 2019

Ovo Ofigo, ya ce har idan shugaba Buhari zai kara tsayawa takaran shugaban kasa a 2019 ya kamata ya dauki wasu batutuwa da Obasanjo ya fada a wasikar da ya rubuta masa da muhimmanci.

KU KARANTA : Manoma miliyan 12m suka samu aikin yi a cikin wannan lokaci - Lai

Obasanjo ya shawarci, Buhari kada ya kara tsayaw takara shugaban kasa saboda zargin rashin iya aiki da nuna bangaranci a mulkin sa.

Ovo Ofigo, ya ce, Buhari zai iya neman takara amma wasikar Obasanjo wata damace da zai sa ya kara gyara siyasar sa.

Wasikar Obasanjo zai kara inganta samun nasara Buhari a zaben 2019,

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng