Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

  • Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna a yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda yan takara
  • Dan takarar kujerar gwamna karkashin APC a jihar ta Kaduna, Alhaji Sani Sha’aban, ya soki tsarin da aka bi wajen zabar deleget din jam’iyyar a jihar
  • Ya aika rubutaciyyar takarda zuwa ga uwar jam’iyya ta kasa inda yake kalubalantar lamarin tare da neman ta saka baki ciki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress( APC) a jihar Kaduna, Alhaji Mahmood Sani Sha’aban, ya soki tsarin da aka bi wajen samar da deleget din jam’iyyar 2,619 a jihar.

Sha’aban wanda ya kasance surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ta shigo lamarin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

Ku tuna cewa kwamitin daukaka kara na tarukan wakilan jam’iyyar a jihar Kaduna ya amince da taron a karshen makon da ya gabata.

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari ya yi watsi da jerin deleget din jam’iyyar
Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari ya yi watsi da jerin deleget din jam’iyyar Hoto: Umar Rabiu, All Progressives Congress - APC
Asali: Twitter

Misis Tinuke Gbadejo-Ogunrinde, shugabar kwamitin daukaka karar ta sanar da manema labarai cewa jimillar deleget 1,275 aka zaba kowanne a matakin karamar hukuma da jiha yayin da aka zabi 69 a matakin tarayya, wanda gaba daya suka zama 2,619.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce:

“An yi zaben ne ta hanyar maslaha daidai da tsarin zabe na APC da kundin tsarin mulki, ba a samu kowani korafi ba a kafin, lokaci da kuma bayan tarukan."

Sani Sha’aban ya soki tsarin fitar da deleget din jam'iyyar a jihar

Kasa da awa daya bayan jawabin Tinuke, Sani Sha’aban ta hannun babban daraktan kamfen dinsa, Dr Danladi Ephraim yace ba a yi zaben fidda deleget da ya samar da wakilai 2,619 ba a koina a jihar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

A cewarsa, samar da sakamakon zaben deleget din kawai aka yi, don haka an tauye yancin dubban mambobin jam’iyyar APC a jihar na son zama deleget kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Sabanin hasashen kwamitin cewa babu kowani korafi, kwamitin yakin neman zaben Sani Sha’aban ta gabatar da wani korafi wanda kwamitin ya ki amsa.

“Wannan sanarwar martani ne kai tsaye ga jawabin batarwa da kwamitin daukaka karar zaben fidda deleget ya fitar.

“Muna son karyatawa a idon ku da idon duniya cewa ba a gudanar da zaben fidda deleget ba a gaba daya jihar Kaduna.

“Mun gabatar da wani korafi ga kwamishinan zabe na INEC a jihar Kaduna kan cewa ba a yi zaben fidda delegt don samar da wakilan jam’iyyar ba, wanda muka gabatar maku da kwafinsa.”

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

Kara karanta wannan

2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC

A wani labarin, sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya bayyana cewa masarautarsa za ta marawa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo baya tare da saka shi a addu’a don Allah ya daura shi kan kujerar shugabancin Najeriya a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa sarkin ya dauki wannan alkawarin ne yayin da ya tarbi mataimakin shugaban kasar, wanda ya kai ziyarar ban girma fadarsa da ke Damaturu, babbar birnin jihar Yobe a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng