Ganduje ya yi alkawarin ba Shugaban Majalisa goyon bayan samun tikitin Shugaban kasa

Ganduje ya yi alkawarin ba Shugaban Majalisa goyon bayan samun tikitin Shugaban kasa

  • Sanata Ahmad Lawan ya ce rade-radin janye takararsa a zaben shugaban kasa ba gaskiya ba ne
  • Shugaban majalisar dattawan zai shiga zaben fitar da gwani, kuma yana sa ran nasara a APC
  • Ahmad Lawan ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fito daga bakin kakakinsa, Iyke Ekeoma

Kano - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya karyata labaran da ake ji na cewa ya hakura da takarar kujerar shugaban kasa a APC.

Daily Trust ta ce Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan bayani ne ta bakin kakakin kwamitin yakin neman takarar shugaban kasar da yake yi, Iyke Ekeoma.

A wani jawabi da aka fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu 2022, Mista Ekeoma ya ce Ahmad Lawan ba zai nemi takarar kujerar ‘dan majalisa a Yobe ba.

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

“Mutanen Najeriya su yi watsi da karyar da wasu suke yadawa domin jan hankalin shugaban majalisar dattawa…
…wajen kokarinsa na cin gadon shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa mai zuwa da za ayi.”

- Iyke Ekeoma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawan kasar ya sha alwashin shi ne wanda jam’iyyar APC mai mulki za ta tsaida a matsayin ‘dan takararta na zama shugaban kasa.

Shugaban Majalisa
Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan Hoto: Tope Brown
Asali: UGC

Sanatan na Arewacin Yobe ya zama ‘dan majalisa mai wakiltar Gashua ne a 1999. Tun shekarar 2007 aka zabe shi a matsayin Sanata a karkashin ANPP.

Lawan ya dura Kano

Jaridar ta ce da yake jawabi wajen ganawa da ‘ya ‘yan APC a jihar Kano, Dr. Lawan ya roki Gwamna Abdullahi Ganduje da ‘yan APC su mara masa baya.

Lawan ya bukaci duka ‘ya ‘yan jam’iyyar APC 500 masu kada kuri’a a zaben tsaida gwani da ake da su a Kano, su ba shi kuri’arsu domin ya tsaya neman takara.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

“Ina son duk kuri’unku 500. Kai, Mai girma Gwamna, ina neman duka masu kada kuri’a 500. Idan ba zan iya samun kuri’u 500, ku bari in samu akalla 400.”

- Ahmad Lawan

A jawabinsa, Gwamna Ganduke ya ce mutanen Kano sun san da nagartar Lawan da gudumuwar da ya bada a siyasa, ya ce za su ba shi cikakkiyar goyon baya.

Sai dai ba za a iya fahimtar abin da gwamnan yake nufi da goyon baya ba. An rahoto Sanatan yana cewa zai yi kokarin ganin shi ne ya samu tutar jam'iyya.

Sanatoci sun ci taliyar karshe

Ku na da labari cewa akwai ‘Yan Majalisar Dattawan da hasashe ya nuna ba za a gansu bayan watan Mayun 2023 ba, watakila har da shi shugaban Majalisar.

Wasunsu za su yi takarar kujerar shugaban kasa ko Gwamna, wasu ba za su samu tikiti ba, wasu sun samu sabani a jam'iyya, wasu kumasun hakura da takarar.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel