Kujera na rawa: Sanatoci 12 da watakila ba za su koma Majalisar Dattawa bayan 2023 ba

Kujera na rawa: Sanatoci 12 da watakila ba za su koma Majalisar Dattawa bayan 2023 ba

  • Akwai ‘Yan Majalisar Dattawan da hasashe ya nuna ba za a gansu bayan watan Mayun 2023 ba
  • Ba dole ba ne a kaddamar da majalisa mai zuwa tare da wadannan Sanatoci da adadinsu ya kai 30
  • Wasunsu za su yi takarar Gwamna, wasu ba za su samu tikiti ba, wasu sun samu sabani daga gida

A wani bincike da Daily Trust tayi kuma ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu 2022, ta ce za a rasa Sanatoci kusan 30 a shekara mai zuwa.

Ga jerin Sanataocin nan, kamar yadda mu ka tsakuro, sannan mu ka hada da na mu nazarin.

Sanatocin da za su yi takarar Gwamna:

1. Enyinnaya Abaribe (Abia)

2. Aishatu Dahiru Binani Ahmed (Adamawa)

Kara karanta wannan

Abinda ya kamata ka sani game da mutum 23 ke son gadon Buhari karkashin APC

3. Albert Bassey Akpan (Akwa Ibom)

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

4. Gershom Bassey (Cross River)

5. Sandy Onor (Cross River)

6. Ovie Omo-Agege (Delta)

7. James Manager (Delta)

8. Obinna Ogba (Ebonyi).

9. Ike Ekweremadu (Enugu)

10. Mohammed Sabo Nakudu (Jigawa)

11. Uba Sani (Kaduna)

12. Yahaya Abdullahi (Kebbi),

13. Teslim Folarin (Oyo)

14. Dimka Hezekiah Ayuba (Plateau)

15. George Sekibo (Rivers)

16. Ibrahim Gobir (Sokoto)

17. Emmanuel Bwacha (Taraba) da

18. Yusuf A. Yusuf (Taraba).

Manyan Sanatocin da za a iya yin waje da su:

1. Adamu Aliero (Kebbi)

Kujerar Muhammad Adamu Aliero ta na rawa domin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu yana kokarin dawowa kan kujerar Sanatan Kebbi ta tsakiya da ya bari.

2. Aliyu Sabi Abdullahi (Neja)

Zai yi wahala Sanatan Neja ta Arewa watau Aliyu Sabi Abdullahi ya samu wa’adi na uku a majalisa domin Gwamna Abubakar Sani Bello ya na harin kujerar.

3. Peter Nwaoboshi (Delta)

Sauya-shekar Peter Nwaoboshi daga PDP zuwa APC ta nuna bai tare da Gwamna Ifeanyi Okowa. Masu hasashe su na ganin Ned Nwoko ne zai doke Nwaoboshi a 2023.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin APC da na PDP da basa neman zarcewa a 2023

Shugaban Majalisar Dattawa
Ahmad Lawan wajen kamfe Hoto: @TheSenatePresident
Asali: Facebook

4. Ibrahim Danbaba (Sokoto)

Shi ma Ibrahim Danbaba ya bar APC saboda sabaninsa da Gwamnansa. Bugu da kari ana tunanin Aminu Tambuwal zai nemi Sanata idan ya rasa tikitin Shugaban kasa.

5. Chukwuka Utazi (Enugu)

Akasin abin da ke faruwa a Neja, Sanata Chukwuka Utazi ya hakura da tazarce a zabe mai zuwa domin Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi yana son wakiltar Enugu ta Arewa.

6. Nora Ladi Daduut

A kudancin Filato haka abin yake, Gwamna Simon Lalong ya saye fam. Ana hasashen cewa Gwamnan zai maye gurbin Ladi Daduut wanda ba ta dade a kujerar ba.

7. Emmanuel Orker Jev (Benuwai)

Kamar dai a irinsu Enugu, Filato da sauransu, a Benuwai ma Gwamna mai barin-gado, Samuel Ortom zai yi takarar Sanata, zaman Sanata Orker Jev ta kare a majalisa.

8. Enyinnaya Abaribe (Abia)

Burin Sanatan Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe shi ne ya zama Gwamna. Rahoton ya ce PDP ta Abia babu zaman lafiya tsakanin Sanatan da Gwamna Okezie Ikpeazu.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban ƙasa a APC da suka sayi Fom N100m kuma suka gaza maida wa

9. Abdullahi Danladi Sankara (Jigawa)

Haka zalika babu tabbacin cewa Abdullahi Danladi Sankara zai zarce. Duk da ya saye fam din shugaban kasa, babu mamaki Gwamnan Jigawa ya nemi Sanata a APC.

10. Emmanuel Bwacha (Taraba)

Sanata Kudancin Taraba, Emmanuel Bwacha ya bi sahun Danbaba da Nwaboshi ya bar PDP saboda takarar Gwamna. Da alama Bwacha ba zai koma majalisa ba.

11. Ike Ekweremadu (Enugu)

Ike Ekweremadu ya na so ya karbi mulkin jihar Enugu a zabe mai zuwa. Babu mamaki zaman Sanatan na Enugu ta yamma a majalisa ya zo karshe bayan shekaru 20.

12. Ahmad Lawan (Yobe)

Idan Ahmad Lawan ya samu tikitin shugaban kasa a APC, shi ma zamansa a majalisa zai kare bayan shekaru 20. Shugaban majalisar dattawan ya na hangen Aso Rock.

Asali: Legit.ng

Online view pixel