2023: Buhari Muke Jira Ya Faɗa Wanda Ya Ke Son a Ba Wa Takarar Shugaban Ƙasa, Mu Yi Biyayya, Zulum

2023: Buhari Muke Jira Ya Faɗa Wanda Ya Ke Son a Ba Wa Takarar Shugaban Ƙasa, Mu Yi Biyayya, Zulum

  • Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno ya ce deleget din jiharsa za su zabi duk dan takarar shugaban kasa da Buhari ya zaba ne
  • Zulum ya bayyana hakan ne yayin tarbar Rotimi Amaechi, yayin da ya ziyarci jihar domin neman goyon bayan deleget din na Jihar Borno
  • A bangarensa, Amaechi ya yi alkawarin cewa idan har aka zabe shi shugaban kasa zai kawo karshen rashin tsaro a arewa maso gabas da Najeriya baki daya

Jihar Borno - Babagana Zulum, gwamnan Jihar Borno, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai taka muhimmin rawa wurin zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, rahoton The Punch.

Yayin tarbar Rotimi Amaechi, dan takarar shugaban kasa a Maiduguri, ranar Lahadi, Zulum ya ce deleget din APC a jiharsa suna jiran shawara daga Buhari kan wanda za su zaba.

Kara karanta wannan

Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewa Ba a APC

Zulum: Buhari Zai Taka Muhimmin Rawa Wurin Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa a APC
Zulum: Buhari Zai Taka Muhimmin Rawa Wurin Zaben Magajinsa a APC. Hoto: Fadar Shugaban Najeriya.
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar na bukaar dan takara wanda zai iya bawa APC dama ta cigaba da rike mulkin kasa a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muna jiran shawara daga Buhari kan wanda za mu zaba a 2023 - Zulum

"Deleget din Jihar Borno za su zabi wanda ya kwanta musu a rai ne. Amma, shugaban mu, Muhammadu Buhari, zai taka muhimmin rawa a wannan lamarin," in ji shi.
"Har yanzu muna jiran shi ya fada mana abin da za mu yi kuma za mu yi biyayya. Shawararsa na da muhimmanci sosai a wurin mu don haka za mu jira mu ji daga gare shi.
"Yan Najeriya su yi addu'a Allah ya basu shugaba na gari, ko daga kowacce kabila ko yanki ne amma dan takarar da zai tabbatar APC ta ci zaben shugaban kasa a 2023."

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Zan kawo karshen kallubalen tsaro a arewa maso kudu da Najeriya baki daya idan aka zabe ni shugaban kasa - Amaechi

A bangarensa, Amaechi ya ce idan aka zabe shi zai kawo karshen matsalar rashin tsaro a kudu maso gabas da kasa baki daya kamar yadda The Cable ta rahoto.

"A lokacin ina gwamnan Jihar Rivers, Buratai shine kwamandan Birgade yayin da Abba Suleiman na kwamishinan yan sanda," in ji shi.
"Mun tabbatar dadazon matasa sun dena zaman kashe wando ta hanyar basu ayyukan yi hakan yasa suka dena gararamba a tituna."

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164