SDP ta bayyana abun da za ta duba kafin ta baiwa Tinubu da sauran yan siyasa tikitinta
- Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar SDP ta gindaya wasu sharudda kafin ta amince da yan siyasar da za su sauya sheka zuwa cikinta
- SDP ta bayyana cewa ba za ta baiwa kowani dan siyasar da ke makale da guntun kashi a tsuliyarsa tikitin takararta ba a zabe mai zuwa
- Ana dai rade-radin cewa Tinubu da wasu yan siyasa za su sauya sheka zuwa SDP idan har jam'iyyarsu ta hana su tikitin takara bayan zaben fidda gwani
Lagos - Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta gindaya wasu sharudda kafin ta amince da jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da jiga-jigan sauran jam’iyyun siyasa da ka so yin amfani da dandamalinta.
Mukaddashin shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Cif Supo Shonibare, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a gefen taron jam’iyyar da aka yi a Lagas.
Daily Trust ta rahoto cewa ana rade-radin wasu yan takarar APC da na PDP na iya sauya sheka daga jam’iyyunsu zuwa wata idan suka gaza samun tikitin takara.
Daya daga cikin yan takarar shugaban kasa wanda ake rade-radin cewa zai iya komawa SDP don cimma kudirinsa shine Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasu magoya bayan Tinubu sun shawarce shi da ya tanadi ‘zabi na biyu’ koda bai samu tikitin APC don cimma daddadiyar kudirin nasa ba.
Sai dai kuma, SDP wacce ake ganin ita ce mafita ta bayyana cewa jam’iyyar ba za ta zama kara zube ga kowani irin dan takara ba.
Da aka tambaye shi game da Tinubu, mukadasshin shugaban na kasa ya yi bayanin cewa yayin da jam’iyyar ke maraba da kowani dan siyasa daga sauran jam’iyyun, wadanda za ta amince da su dole su zamo mutane masu mutunci wadanda basu da guntun kashi a tsuliyarsu.
Ya ce:
“Muna maraba da mutane daga sauran jam’iyyun siyasa wadanda ke ganin ba ayi masu adalci ba a jam’iyyunsu na yanzu, amma ba za mu zama abin dogaro ga masu son rai ba, wadanda a ganinmu suna cikin matsalar Najeriya.
“SDP ba za ta zama mafakar PDP ko APC ba, saboda haka mai zai sa mu dunga gabatar da kanmu a matsayin zabi na biyu."
Shugaban jam’iyyar ya yarda cewa akwai yan takara masu mutunci sosai a APC da PDP kuma sune za a yi maraba da zuwansu jam’iyyar.
Ya ce:
“Ba za mu yi maraba da mutanen da aka yankewa hukunci ba koda sun ce suna daukaka kara kan hukuncin, ba za mu yi maraba da mutanen da ke da shari’a a kotu ba koda ba a tantance lamarin ba.
“Idan a binciken farko, muka duba lamuransu muka ga cewa akwai zarge-zarge a kansu, saboda muna da wani kwamiti na lauyoyi, idan suka duba zarge-zargem. Musamman idan an tuhume su, kuma ba a yankewa mutum hukunci ba, ba za mu gabatar da irin wadannan mutane a matsayin wadanda za su daga tutarmu ba."
Shugaban jam’iyyar ya ce SDP na da damar nasara sosai a zabe mai zuwa duba ga gazawar APC da PDP tsawon shekaru fiye da 20 da suka yi kan mulki.
Shonibare ya kuma yi zargin cewa akwai tawaga da suka kutsa kai cikin jam’iyyar SDP saboda irin damar da take da shi a yayin da suke kokarin kwace ta daga hannun wadanda suka kafa ta.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta dogara ne kan shari’o’in da ke gaban kotu don taimaka mata wajen shawo kan wannan kalubale.
Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya
A gefe guda, wani rahoto da jaridar BusinessDay ta buga na nuni da cewa, Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar APC, ya fara tuntubar jam’iyyar SDP, a matsayin wata hanyar da zai bi wajen tabbatar da aniyarsa ta gaje Buhari, idan APC ta kasa ba shi tikitin takara.
A cewar rahoton, majiyoyi na kusa da SDP sun ce Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar a kwanan baya domin neman ma kansa masaukin siyasa.
Matakin da Tinubu ya dauka, an ce ya samo asali ne sakamakon lamarin da ya kai ga fitar da ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC da wasu mukamai a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.
Asali: Legit.ng