Tsohon Dogarin Abacha, Hamza Al Mustapha zai fadi mutum 56 da suka hana kasaa cigaba

Tsohon Dogarin Abacha, Hamza Al Mustapha zai fadi mutum 56 da suka hana kasaa cigaba

  • Hamza Al-Mustapha ya zargi wasu mutane da ba su wuce 50 ba da hana kasar nan cigaba har yau
  • Tsohon Sojan ya bayyana cewa ya samu wannan bayani ne a lokacin da yake garkame a gidan yari
  • Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya yi zaman gidan kaso na kimamin shekara 16 a Najeriya

Kaduna - Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya wanda ya yi aiki a matsayin babban dogarin Janar Sani Abacha ya zargi wasu da hana kasar nan sakat.

Da gidan BBC Hausa ya yi hira da Manjo Hamza Al-Mustapha a garin Kaduna, ya bayyana cewa mutane 56 rak ne suke gwagwuyar Najeriya tamkar wasu gara.

Hamza Al-Mustapha ya ce a lokacin da yake tsare, ya sha bakar wahalar da ta kai ya cire tsammanin zai rayu, ya iya kawo zuwa wannan lokaci a raye.

Kara karanta wannan

Mutum 56 kacal ke hana ruwa tafiya a Najeriya, Manjo Hamza Al-Mustapha

Tsohon sojan kasan yake cewa a sa’ilin da yake garkame ne ya fahimci akwai wasu gungunan mutane 56 daga lungunan kasar nan da suka hana a cigaba.

Vanguard ta rahoto Manjo Al-Mustapha yana cewa wadannan daidaikun mutane sun fi Najeriya dukiya, kuma da za su matsa gefe, da kasar ta samu nasarori.

Manjo Al-Mustapha yana takara

A cewar Hamza Al-Mustapha, idan ya karbi shugabanci a 2023, zai dauki tsuttsauran matakan da za su yi sanadiyyar kawo sauyi a halin da al'umma su ke ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Dogarin Abacha
Manjo Hamza Al Mustapha Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Daily Trust ta ce mai neman takarar shugaban kasar a karkashin jam'iyyar adawa ta AA, ya yi alkawarin daukar mataki ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.

Su wanene wadannan mutane?

Har Al-Mustapha ya gama bayanin na sa, bai kama sunayen wadannan mutane da yake zargin sun tasa kasar a gaba ba, sai dai ya yi alkawarin kawo sauyi.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Da yake gidan yari ne ya ce ya samu labarin gungun wadannan mutane da suka gagari kowa. Ya ce idan lokaci ya yi, zai fadawa Duniya sunayen mutanen.

Bayan Janar Sani Abacha ya rasu a kan kujerar shugaban kasa, dogarin na sa ya yi shekara da shekaru a gidan yari bisa zargin da suka hada da kisan kai.

A shekarar 2013 aka fito da Al-Mustapha daga gidan yarin kirikiri da ke Legas. Tun Oktoban 1998 aka tsare Dogarin. A karshe kotu ta wanke shi daga zargi.

Zaman 'Yar'adua shugaban kasa

A yau kun ji yadda Olusegun Obasanjo a lokacin yana shugaban kasa ya dauko wanda zai karbi mulki daga hannunsa bayan ya gagara sake zarcewa a 2007.

Olusegun Obasanjo ya kafa wani kwamitin mutum tara da aka daurawa nauyin tallata Umaru 'Yar'adua a lokacin yana shirin sauka daga Gwamnan Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel