Takarar Shugaban Ƙasa: Na Fi Kowa Cancanta, Ina Cin Garin Kwaki Sau 3 a Kullum, Amaechi

Takarar Shugaban Ƙasa: Na Fi Kowa Cancanta, Ina Cin Garin Kwaki Sau 3 a Kullum, Amaechi

  • Tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi ya ce ya fi ko wanne dan takara gogewa da kuma cancanta
  • Ya bayyana wa wakilan jam’iyyar APC hakan ne a Jihar Neja a ranar Alhamis inda ya ce zai fi fahimtar talakawa musamman idan aka duba cewa iyayensa talakawa ne
  • Ya ci gaba da cewa zai fi saukin alaka da talakawa kamar yadda ya saba cin garri sau uku a ko wacce rana kuma har yanzu bai dena ba

Neja - Rotimi Amaechi, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC kuma tsohon ministan sufurin ya ce ya fi ko wanne dan takara sanin makamar aiki musamman idan aka kalli cewa asalinsa talaka ne fitik.

The Punch ta ruwaito cewa ya yi wannan bayanin ne yayin ganawa da wakilan jam’iyyar APC a Jihar Neja kasancewar zaben fidda gwani ya na kara matsowa.

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Takarar Shugaban Ƙasa: Na Fi Kowa Cancanta, Ina Cin Garin Kwaki Sau 3 a Kullum, Amaechi
2023: Na Fi Kowa Cancanta, Ina Cin Garin Kwaki Sau 3 a Kullum, Amaechi. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Ya ce sai ya fi saukin hada kai da talakawa saboda dama can a ko wacce rana ya na cin garri sau uku kuma har yanzu ma hakan ne.

Tsohon ministan ya ce duk da gogewarsa ta baya wacce ya rike mukamai kamar kakakin majalisa, gwamna, minista da kuma darekta-janar na kamfen din shugaban kasa har sau biyu, amma akwai bambanci sosai tsakaninsa da sauran ‘yan takara saboda shi mutum ne mai jama’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce iyayensa talakawa ne

“Wani babban bambancin da ke tsakanina da su shi ne ni dan siyasa ne, su kuma ba hakan ba ne. Ni zan iya zuwa gare ku baki-da-baki in yi muku magana,” a cewarsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa iyayensa talakawa ne hakan ya sa ya samu damar fahimtar halin da jama’a su ke ciki.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Ya ci gaba da cewa:

“Zan iya saurin kulla alaka da mutane. Iyaye na ba masu kudi ba ne. Mahaifina talaka ne kuma mahaifiyata ko turanci mai kyau ba ta ji. A baya na ci garri sau uku a rana kuma har yau ina cin garri sau uku a ko wacce rana, don haka na san talauci.”

Ya sanar da mutanen Neja cewa ya fahimci matsalarsu ta rashin tsaro kuma ya san hanyar da zai iya kawo karshenta a jihar.

Ya tunatar da yadda ya goyi bayan Buhari duk da dan arewa ne

A cewarsa:

“Na san kuna wahala, na taba rike kujerar gwamnan Jihar Ribas lokacin ana garkuwa da yara haihuwar watanni biyu, ban taba barci ba har sai na tabbatar kowa ya yi bacci.
“Kuma a cikin watanni biyu na gama da rashin tsaro a Jihar Ribas.”

Ya roki mutanen arewa da sauran ‘yan Najeriya su mara masa baya saboda kokarin da ya yiwa kasar nan lokacin da ya goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da kallon dan arewa ne shi ko kudu ba ne.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

Ya bayyana kalubalen da ya fuskanta inda ake ta cewa ya na goyon bayan Hausa/Fulani amma duk da haka ya toshe kunnuwansa.

2023: Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel