An kuma: Dumi a inuwa Ganduje yayin da wani kwamishinansa ya koma NNPP

An kuma: Dumi a inuwa Ganduje yayin da wani kwamishinansa ya koma NNPP

Kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano, Shehu Na’Allah Kura, ya yi murabus daga mukaminsa a karkashin mulkin Ganduje.

Rahoton da muka samo daga jaridar Leadership ya ce, daga karshe dai Kura ya koma jam’iyyar NNPP mai tashe a yanzu a jihar ta Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Murabus din Kura daga inuwar Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ma’aikatan gwamnan, Ali Haruna Makoda ya yi murabus, wanda daga baya ya koma jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

A cewar Garba, an nada Kura a matsayin kwamishinan ma’aikatar kudi ne bisa bukatar tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau, bayan zaben 2019.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Daya daga cikin kwamishinonin da Sanata Ibrahim Shekarau kawo a gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ma’aikatar kudi da bunkasa tattalin arziki, Shehu Na’Allah Kura ya yi murabus ya koma tsagin ubangidansa."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan ya kara da cewa har zuwa lokacin da Shekarau ya koma NNPP, Kura dan jam’iyyar APC ne, kuma ya taba rike mukamin kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel