'Dan takarar PDP ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara gyara Najeriya yadda ake sa rai

'Dan takarar PDP ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara gyara Najeriya yadda ake sa rai

  • Bala Mohammed ya yi bayanin abin da yake tunani ya kawowa Muhammadu Buhari cikas a mulki
  • ‘Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce Buhari soja ne wanda bai fahimci yadda ake siyasa ba
  • Gwamnan na Bauchi ya ce shugaban kasar ya gagara gane ba mutanen kwarai su ke tare da shi ba

Katsina - ‘Dan takarar shugaban Najeriya kuma gwamnan Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed yana ganin Muhammadu Buhari bai fahimci siyasa ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu 2022, da ya nuna cewa Bala Abdulqadir Mohammed ya kai ziyara zuwa jihar Katsina.

Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya ziyarci jihar shugaban kasar ne da nufin samun goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a zaben fitar da 'dan takara.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

Da yake jawabi a jiya, gwamnan ya fadawa taron ‘yan adawar cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gagara kawo gyaran da al’umma su ka sa ran gani.

Mai girma Gwamna yake cewa shugaban kasar ya samu matsala ne saboda mayaudara suka zagaye shi.

Bangaren jawabin Bala Mohammed

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mutanen Katsina sun yi abubuwa na kawo cigaban kasar nan, misali, abin da Marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yi wa Najeriya. Allah ya jikan shi.”
'Dan takarar PDP da Buhari
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed da Muhammadu Buhari Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

“Amma abin takaici, ‘dan ku, ubanmu, shugaban kasa mai ci, zagaye yake da mutane marasa gaskiya, makaryata da ya ke tunanin mutane masu daraja ne.”
“Saboda shi soja ne, bai san halin mutane ba, ko bai fahimci harkar siyasa ba.”
“Mun san kowane irin mutum, na kirki da na banza, dole ne mu canza wannan tunanin na cewa kowa mutumin banza ne, dole mu ceci ‘ya ‘ya da jikokinmu.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

- Bala Mohammed

An rahoto Bala Abdulqadir Mohammed yana cewa akwai bukatar irinsa ya karbi mulkin Najeriya.

Na kawo sauyi a Bauchi – Bala

Premium Times ta ce Mohammed ya yi bayanin irin yadda ya kawo zaman lafiya a jiharsa ta Bauchi ta hanyar zama da sarakunan gargajiya da kuma malamai.

Mai neman tikitin na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa a cikin shekaru hudu, gwamnatinsa ta samu manyan nasarori a bangaren kiwon lafiya da ilmi a Bauchi.

Osinbajo bai yi kasuwa a Jigawa ba?

Ku na da labari cewa a karshen makon da ya gabata ne Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara zuwa jihar Jigawa inda ya zauna da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a garin Dutse.

Amma sai aka ji Osinbajo bai samu damar haduwa da Gwamna Badaru Abubakar da Mataimakinsa ba, kuma bai iya haduwa da Sarkin Dutse a fadarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel