Rikicin siyasar Kano: Garo na shirin barin APC duk da zabarsa da aka yi ya gaji Gawuna
- Rikicin siyasar Kano na kara daukar wani salo yayin da wanda ka zaba ya gaji mataimakin gwamna ke shirin barin APC
- Wannan na zuwa ne daga wasu majiyoyin da suka yi imani da cewa, Garo na jin haushin wasu abubuwa a jam'iyyar ta APC
- Tun farkon kada gangar siyasa Kano ke ganin sabbin lamurra a siyasa, inda siyasra jihar ke jan hankalin jama'a a kasar nan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kano - A halin yanzu dai wani rikici ya sake kunno kai a APCn jihar Kano, yayin da rahotanni ke cewa dan takarar mataimakin gwamna Murtala Sule Garo da Ganduje ya zaba yana shirin sauya sheka.
Garo, wanda shine tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zabe shi tare da mataimakin gwamna na yanzu, Nasir Gawuna don su taka rawa a zaben 2023 mai zuwa.
Sai dai kuma bayan zaman sulhu da aka yi tsakanin Ganduje da Sanata Barau Jibrin, babban dan adawar siyasar Garo daga shiyyar Kano ta Arewa, an ce Garo bai ji dadi ba, rahoton Daily Trust.
Ganduje ya amince da barwa Barau tikitin takarar sanatan Kano ta Arewa bayan da Sanatan ya yi watsi da burinsa na takarar gwamna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin da yasa Garo ke shirin barin APC
Majiyoyi sun ce Garo na da 'yar tsama da Barau, baya ga kasancewarsa abokin adawa na siyasa, ya taka rawar gani a matsayin daya daga cikin shugabannin kungiyar G-7 da ke kokarin kwace ikon jam’iyyar daga tsaginsu.
An ce, Garo na jin bai kamata a yi maraba da Barau ga sansanin su Ganduje ba, bayan da kotun koli ta yanke hukuncin sanya jam'iyyar a hannun gwamnan.
An tattaro cewa gwamnan da Barau sun ziyarci Garo a gidansa da tsakar daren Laraba domin sasanta batutuwan tare da yin watsi da shirinsa na jefar da tikitin takara da jam’iyyar.
Sai dai wasu majiyoyi na kusa da tsohon kwamishinan sun ce ko bayan kammala taron, Garo bai da tabbas game da shirin sauya sheakr, kuma ya ki bayar da tabbatacciyar amsa kan bukatar su Ganduje.
Daily Trust ta kara da cewa, wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
"Yana shirin ganawa da abokanansa da kuma yanke shawara ta zahiri, amma har yanzu yana da haushin ci gaban da aka samu (dawowar Barau fagen daga) amma bai yi watsi da tikitin takara ba."
Har ila yau, an ce Garo ya damu matuka kan rikicin sauya shekar da jam’iyya mai mulki ke gani a Kano, wanda da dama ke ganin zai iya shafar karfin jam’iyyar a 2023.
An kuma tattaro cewa, watakila Garo na tunanin komawa jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso mai kayan dadi, wacce ta fara tasowa a Kano, kuma ta janyo jiga-jigan jam’iyyar APC da dama ciki har da Sanata Ibrahim Shekarau zuwa inuwarta.
Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso, surukin Garo ne kuma ya taka rawa wajen gina shi a matsayin gogaggen dan siyasa a jihar.
Kwankwaso ne ya shigo da shi siyasar Kano a matsayin sakataren jam’iyyar PDP a shekarar 2007.
‘Dan Kwankwasiyya ya jefar da jar hula, ya koma APC, daga hana shi takara a Jam'iyyar NNPP
A wani labarin, siyasar Kano ta na cigaba da rikida tun da Rabiu Musa Kwankwaso ya bada sanarwar ficewarsa daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP a watan Maris.
A ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, jam’iyyar NNPP ta zabi wadanda za su tsaya mata a matsayin ‘yan takara a jihar Kano a zaben shekara mai zuwa.
Legit.ng Hausa wannan zabi da aka yi ya bar baya da kura a siyasar Kano, inda wasu cikin ‘yan siyasan da suka saye fam su ke ganin ba ayi masu adalci ba.
Asali: Legit.ng