An Dakatar Da Shugaban PDP Na Jihar Zamfara Kan Cin Dunduniyar Jam'iyya

An Dakatar Da Shugaban PDP Na Jihar Zamfara Kan Cin Dunduniyar Jam'iyya

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen Jihar Zamfara ta dakatar da shugabanta Kanal Bala Mande (mai murabus)
  • Hakan na zuwa ne sakamakon korafin da aka shigar kansa na zarginsa da sayar da sirrikan jam'iyya da wasu abubuwa da suka saba dokar jam'iyya
  • Tuni dai an kafa kwamitin bincike na musamman da za ta duba zargin da ake masa cikin wata guda sannan ta bada rahoto

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar PDP ta Jihar Zamfara ta sanar da dakatar da shugabanta na Jihar, Bala Mande, har sai an kammala bincike da ake yi kan zarginsa da sayar da sirrin jam'iyyar ga wasu mutane don biyan wasu bukatun kansa.

A cewar sanarwa sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Abba Bello, ya fitar, ya ce an dakatar da shugaban jam'iyyar ne kan zargin cin amanar jam'iyya da wasu abubuwan, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

An Dakatar Da Shugaban PDP Na Jihar Zamfara Kan Cin Dunduniyar Jam'iyya
An Dakatar Da Shugaban PDP Na Jihar Zamfara Kan Cin Amanar Jam'iyya. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta kara da cewa:

"Hakan ya zama dole domin shugaban jam'iyyar ya rika gudanar da ayyukan jam'iyya ta ba tare da kwamitin ayyuka ba, yana sayar da sirrika ga duk wanda zai biya shi kudi."

Sanarwar ta ce abin da ya aikata sun saba wa sassa daban-daban na kundin tsarin mulkin jam'iyyar ta PDP.

Ta kara da cewa, "Ya zama dole domin dakile kada Kwanel Mande (mai murabus) ya yi amfani da karfin ikon ofishinsa ba ta yadda ya dace ba da saba dokokin jam'iyyar.
"Dakatarwar ta wata daya ne, wannan zai bawa kwamitin ayyuka dama ta kafa kwamitin bincike kan zargin da ake masa.
"Don haka, mataimakin shugaban jam'iyya, na yankin Kaura Namoda, Mallam Ali Namoda, za cigaba da jagorancin jam'iyyar yayin dakatarwar."

Bello ya ce tuni kwamitin ayyuka ta kafa kwamitin bincike da za ta bincika zargin.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

Mambobin kwamitin sun hada da Ahmed Sani Kaura Ciyaman; Bala Zurmi, Mamba; Sanin Baba, mamba; Abdulhadi Ahmed, mamba; Suwaiba Bako, Mamba; Abul Mustapha, mamba; da Ibrahim Jibril, wanda zai yi aiki a matsayin sakatare.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel