Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

  • Alamu sun nuna cewa babban jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, na iya mallakar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki
  • Tinubu na kara samun gagarumin goyon baya a jihohin arewacin kasar, sannan wakilan jam’iyyar suna la’akari da nasarorin da ya samu
  • Daga cikin abubuwan da suka ba mai neman takarar shugaban kasar fifiko kan sauran shine yadda bai da nuna kabilanci da kuma halinsa na bin tsarin damokradiyya da sauransu

Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na ci gaba da samun garumin goyon baya a takararsa na son mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.

PM News ta rahoto cewa wani bincike daga mabiya jam’iyyar a Kano, Kaduna, Katsina, Neja, Adamawa da wasu yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya nuna cewa babu wani dan takara da wakilai ke ganin mutuncinsa kuma suka yarda da shi kamar Tinubu.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Hakazalika shine ya samu tarba mai kyau sannan aka bayanna shi a matsayin jajirtaccen shugaba kuma dan jam’iyya na gaskiya.

Wata majiya a jihar Katsina ta ce wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na tantance bayanan masu neman takara ta fuskar dimokradiyya, jam’iyyar, hakuri da kuma nasarorin da suka samu, The Nation ta rahoto.

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya
Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya Hoto: The Guardian
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ta ce:

“Ina iya fada maku cewa muna la’akari da Asiwaju baya saboda tarin nasarorinsa. Ko shakka babu shi dan Najeriya ne mara nuna kabilanci wanda ke ci gaba da bin tsarin dimokradiyya da doka tsawon sama da shekaru 30.
“Yan Najeriya da dama sun amfana daga karamcinsa, kuma bashi da son kai wajen hulda da mutane, ba tare da la’akari da kabila, addini da sauran banbance-banbance ba. Idan aka leka iyalan Tinubu, daular siyasarsa da wadanda suka zama manyan mutane a Najeriya a yau ta sanadiyarsa ya isa komai.”

Kara karanta wannan

Tana shirin kwabewa PDP yayin da daruruwan mambobinta suka sauya sheka zuwa APC

Tinubu, a daya daga cikin ziyarar da ya kai arewa, ya ce ya shiga takarar ne domin hada kan kasar, yana mai bayyana cewa yana da abubuwan da ake bukata da gogewa don zama shugaban kasa.

Ya fada ma wakilan cewa yana da gogewar da zai daidaita lamura, musamman a bangaren tattalin arziki da tsaro, don tabbatar da ganin cewa yan Najeriya sun amfana daga albarkatunta.

Wani wakilin jam’iyyar a jihar Kaduna, Haliru Shetimma, ya ce wakilan jihar Kaduna su ne jagora abun yarda a tsakanin yan takarar shugaban kasa domin mara masa baya.

Ya ce:

“Tsohon gwamnan na jihar Lagas baya daya daga cikin wadannan shugabanni na gaggawa wadanda a dare daya suka gano akwai bukatar su zama shugaban kasa. Ga mu da muke Kaduna da sauran jihohi, muna tare da takarar Asiwaju. Ya san hanyar. Muna bibiyar ci gaba a Lagas, inda wadanda ba Yarbawa ba suke zama cikin shugabanni da yan majalisa. Irin wannan shugaban muke so.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Talata, ya ayyana kansa a matsayin mafi cancanta a cikin wadanda ke neman takarar shugaban kasa a 2023.

Saraki ya yi magana ne a Osogbo yayin wata ganawa da shugabanni da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Osun, jaridar Punch ta rahoto.

Dan takarar shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ya kasance kusa da iyalan PDP a jihar, yana mai cewa ya kuma yi aiki tare da su don tabbatar da ganin cewa jam’iyyar adawar ta koma mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng