Tana shirin kwabewa PDP yayin da daruruwan mambobinta suka sauya sheka zuwa APC

Tana shirin kwabewa PDP yayin da daruruwan mambobinta suka sauya sheka zuwa APC

  • Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar PDP ta rasa wasu mambobinta guda 500 a karamar hukumar Ayedaade da ke jihar Osun
  • Bayan sauya shekar nasu, sai suka yada zango a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar
  • Sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne saboda tarin nasarorin da Gwamna Adegboyega Oyetola ya samu tun bayan hawansa mulki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Kimanin mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 500 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Ayedaade.

A wata sanarwa daga babban sakataren labaran gwamnan jihar, Ismail Omipidan, ya ce masu sauya shekar sun alakanta matakin da suka dauka na barin PDP ne saboda tarin nasarorin da Gwamna Adegboyega Oyetola ya samu tun bayan hawansa mulki.

Tana shirin kwabewa PDP yayin da daruruwan mambobinta suka sauya sheka zuwa APC
Tana shirin kwabewa PDP yayin da daruruwan mambobinta suka sauya sheka zuwa APC Hoto: Adegboyega Oyetola
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu sauya shekar sun kasance mambobin kungiyoyin PDP daban-daban a cikin karamar hukumar.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

Da yake magana a madadin masu sauya shekar, Raufu Lukman, ya yi bayanin cewa sun yanke shawarar komawa jam’iyyar APC mai mulki ne saboda gwamnatin Oyetola ta yi kokari sosai a kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Kamar yadda kuke gani, mun zo nan mu da yawa domin janye kanmu daga PDP da kuma sanar da duniya cewa mun koma APC, jam’iyyar da ke nufin al’umma da alkhairi.
“Shawarar da muka yanke na barin tsohuwar jam’iyyar a wannan mawuyacin lokacin ya nuna cewa gwamnati mai ci karkashin jagorancin Gwamna Oyetola ta yi gagarumin kokari a dukkan bangarorin tattalin arziki sannan mun shirya bayar da namu gudunmawar domin ciyar da jiharmu gaba da inganta rayuwar al’ummarmu.
“Da ni da takwarorina da muke mambobin kungiyoyin da suka sauya sheka tsakanin 500 zuwa 550 mun kuduri aniyar yin aiki tare da sauran mutane domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Yayin da yake tarban masu sauya shekar, kwamishinan kudi na jihar Osun, Bola Oyebamiji, ya jinjina masu a kan wannan mataki da suka dauka na komawa APC, rahoton The Nation.

Shugabannin APC sun fara buga lissafin yadda za a fitar da ‘Yan takara a zaben 2023

A wani labarin, mun ji cewa yayin da aka fara shirin zaben fitar da gwani, jam’iyyar APC mai mulki ta soma tattaunawa a kan hanyar da za a bi domin tsaida ‘yan takara.

This Day ta ce ‘yan majalisar aiwatarwa na APC watau NWC su na tattaunawa ta ko ina a fadin kasar nan, a kan maganar fito da wadanda za a ba tutan 2023.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa za a tattauna da masu ruwa da tsaki da wasu shugabannin na kasar nan domin ganin an fito da ‘yan takara masu lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel