Hotuna: Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, kwankwaso ya taya shi murna, NNPP

Hotuna: Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, kwankwaso ya taya shi murna, NNPP

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, sannan sanata mai ci, Ibrahim Shekarau ya canza sheka daga.
  • . jam'iyyar APC zuwa NNPP
  • Hakan yazo ne bayan wasu kwanaki da Abdulmumin Jibrin, tsohon 'dan majalisar dattawa, sannan daraktan kamfen din Bola Tinubu ya koma NNPP
  • An dauki tsawon lokaci ana samun sabani tsakanin Ganduje da Shekarau tun bayan taron jam'iyyar APC a jihar, tsagi biyun sun samar da shugabanni daban-daban a fadin jihar

Kano - Jam'iyyar NNPP ta ce Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano sannan sanata mai ci, ya dawo jam'iyyar.

Cigaban yazo ne bayan wasu kwanaki da Abdulmumin Jibrin, tsohon 'dan majalisar dattawa kuma babban daraktan kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya shiga jam'iyyar, The Cable ta ruwaito.

Sanata Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, Cewar jam'iyyar NNPP
Sanata Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, Cewar jam'iyyar NNPP. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Canza shekar da Jibrin ya yi ta tabbata duk da kokarin da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, yayi don kangeshi daga barin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

A wata wallafa ta shafin Twitter a ranar Talata, NNPP ta ce daga karshe tsohon gwamnan Kano ya koma jam'iyyar, inda ta kara da cewa Kwankwaso ya kai masa "ziyarar taya murnar" wannan cigaban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daga karshe: Sanata Ibrahim Shekarau ya dawo bangarenmu," kamar yadda wallafar Twitter ta bayyana.

Tushen rikicin

An dauki tsawon lokaci ana samun sabani tsakanin Ganduje da Shekarau tun daga lokacin da APC ta gabatar da gangamin taronta a jihar.

Tsagin Ganduje da Shekarau sun samar da shugabanni daban-daban. Tsagin Shekarau ya samar da Haruna Danzago a matsayin shugaban jam'iyyar na jiha, yayin da Abdullahi Abbas yake shugaban tsagin Ganduje.

Sai dai, zaman kotu a babban birnin tarayya (FCT) ya tabbatar da tsagin Shekarau a watan Nuwamba, 2021 - amma kotun daukaka kara da kotun koli sun dade da aje shari'ar a gefe.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kira zaman gaggawa a sakamakon rikicin da ke neman kunnowa APC a Kano

Daga karshe, Shekarau ya shirya haduwa da masu bashi shawarwari da mambobin gundumarsa a ranar Laraba a kan cigaban da aka samu.

Har yanzu, tsohon gwamnan bai sanar da canza shekarsa zuwa NNPP ba.

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

A wani labari na daban, awanni ƙalilan bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai ziyara gidan Sanata Ibrahim Shekarau, domin hana shi komawa NNPP, Jagora Rabiu Musa Kwankwaso ya tura tawagar wakilai.

Kwankwaso, wanda ke shirin karɓan Shekarau zuwa NNPP ranar Asabar, ya samu labarin motsin Ganduje, nan take ya kira gidan Shekarau inda ya sanar musu yana nan tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng