2023: Atiku Ya Fatattaki Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau

2023: Atiku Ya Fatattaki Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a PDP ya umurci hadimansa da jami'ansa tsaro su fatattaki yan jarida daga dakin taro a sakariyar PDP a Plateau
  • Atiku ya ce shi deleget ya zo gani ba 'yan jarida ba don haka hadimansa da jami'an tsaro suka fattaki yan jaridar har wasu suka lalata wayoyinsu da kayan aiki wurin turereniya garin tserewa
  • Yan takarar shugaban kasa da dama sun ziyarci Jihar ta Plateau amma duk cikinsu babu wanda ya umurci a kori yan jarida a yayin da ya zo gana wa da deleget da shugabannin jam'iyya

Dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya fattaki yan jarida daga sakatariyar PDP a lokacin da ya ziyarci jihar a ranar Litinin domin gana wa da shugabannin jam'iyyar na jihar da kuma deleget don tattaunawa kan takararsa na 2023, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

Atiku ne dan takarar na farko da ya fara korar yan jarida daga dakin taron na PDP duk da cewa wasu cikin yan takara a PDP sun ziyarci Plateau a baya-bayan nan.

2023: Atiku Ya Fatattaki Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau
2023: Atiku Ya Kori Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Deleget na zo gani ba 'yan jarida ba, In Ji Atiku

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya isa sakatariyar ta PDP na Plateau misalin karfe 2.19 na rana, amma da ya tarar da yan jarida suna jiransa, ya bada umurnin su fita yana cewa "ba abin da ya hada ni da yan jarida". Deleget na zo gani," kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Wannan umurnin ya sa hadimansa da jami'an tsaronsu suka bazama suka fara fatattakar yan jaridar, hakan ya janyo turereniya, aka yi asarar na'urori ciki har da wayar salula da sandar dora kwamara ta Channels TV.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Adesina Ya Yi Magana Kan Batun Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Jami'an PDP da delegets din sun gaza taimakawa yan jaridar da suka rika tserewa amma ba su ji dadin abin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi ba, duk da ya taba ziyarar jihar a 2019 kuma bai nuna irin wannan fushin ba ga yan jarida da ke aikinsu.

Jihar Plateau na da deleget kimanin 85 amma bayan afkuwar wannan lamarin babu tabbas idan za su mara masa baya a takararsa.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel