Daga Ƙarshe, Adesina Ya Yi Magana Kan Batun Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Daga Ƙarshe, Adesina Ya Yi Magana Kan Batun Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

  • Shugaban Bankin Cigaban Afirka, (AfDB), Akinwumi Adesina, ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na ya fito takarar shugaban kasa a 2023
  • Adesina cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata 17 ga watan Mayu ya ce ya yi godiya bisa kirar da aka masa amma ba zai yi takarar shugaban kasar ba
  • Shugaban na AfDB ya ce a halin yanzu ya mayar da hankalinsa ne wurin taimakawa nahiyar Afirka ta cigaba da bangaren tattalin arziki

Dr Akinwumi Adesina, Shugaban Bankin Cigaban Nahiyar Afirka, (AfDB) ya nesanta kansa daga takarar shugaban kasa na shekarar 2023, rahoton Daily Trust.

Gabanin babban zaben na shekarar 2023, an shawarci Adesina da ya shiga takarar shugaban kasar.

2023: Adesina Ya Yi Ƙarin Haske Game Da Batun Takarar Shugaban Ƙasa
Yanzun Nan: Ba Zan Yi Takarar Shugaban Kasa Ba, Akinwumi Adesina. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

An rahoto cewa wasu kungiyoyi sun siya fom har sun cike sun mayar a madadin Adesina a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa

Sun ce Adesina yana da nagartattun halaye da kasar ke bukata a yanzu domin magance matsalolin da ta ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Adesina ya ce ba shi cikin masu takarar shugaban kasa, ya kara da cewa ya mayar da hankali ne a aikinsa a AfDB.

Sanarwar ta ce:

"Na yi matukar godiya bisa kiraye-kirayen da yan Najeriya na gida da waje suka yi min na fitowa takarar shugaban kasa. Na yi godiya ga dukkan wadanda suka yi sadaukarwa sosai don kashin kansu na yi min tayin.
"Hadakar kungiyoyin matasa,mata, manoma, masu bukata na musamman da sauran yan Najeriya da suka nuna cewa suna son in yi takarar don kashin kansu. Na yi godiya sosai amma aiki na na yanzu ba dai bani damar amsa kirar nan ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

"A yanzu na mayar da hankali wurin aikin ganin cigaban Afrika da yan Najeriya da sauran masu hannun jari a Bankin Cigaban Afirka suka bani. Ina son mayar da hankali kocokan don kawo cigaba da bunkasar Afirka. Allah ya yi wa Najeriya albarka. Amin."

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel