Shugabannin APC sun fara buga lissafin yadda za a fitar da ‘Yan takara a zaben 2023

Shugabannin APC sun fara buga lissafin yadda za a fitar da ‘Yan takara a zaben 2023

  • Shugabannin jam’iyyar APC su na so a samu baki daya wajen tsaida ‘yan takara a zabe mai zuwa
  • ‘Yan majalisar NWC su na zama da jagororin APC daga ko ina domin tantance maganar bada takara
  • APC ta na so a tsaida wadanda ake ganin sun fi kowa cancanta da su tsaya mata takara a Najeriya

Abuja - Yayin da aka fara shirin zaben fitar da gwani, jam’iyyar APC mai mulki ta soma tattaunawa a kan hanyar da za a bi domin tsaida ‘yan takara.

This Day ta ce ‘yan majalisar aiwatarwa na APC watau NWC su na tattaunawa ta ko ina a fadin kasar nan, a kan maganar fito da wadanda za a ba tutan 2023.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa za a tattauna da masu ruwa da tsaki da wasu shugabannin na kasar nan domin ganin an fito da ‘yan takara masu lafiya.

Kara karanta wannan

Sakamakon umarnin da aka bada, mai ba Buhari shawara ya ajiye aiki domin neman Gwamna

Burin jam’iyyar ta APC shi ne ta tsaida ‘yan takarar da zai yi wahala a iya doke su a zaben badi.

A dalilin haka ake so a fito da jerin wadanda za a amince a ba tuta daga jihohi 36. Za ayi wannan ne ba tare da an hana kowa shiga zaben fitar da ‘dan takara ba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, makasudin fito da wadanda za a zaba a matsayin ‘yan takara a zaben fitar da gwani shi ne a tika jam’iyyun hamayya da kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin APC
Shugabannin APC na kasa Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Facebook

Manyan APC su na ta ganawa

Tun a farkon makon nan aka ji cewa wasu Sanatoci masu-ci da gwamnan jiha da wani tsohon Minista sun sa labule a kan yadda za a fito da ‘yan takaran nan.

Ko da jam’iyya ta fi maida hankali wajen sauraron matsayar gwamnoni, shugabannin APC na kasa sun zabi su yi shawara da sauran jagorori a kowane mataki.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

Rahoton ya ce irin haka ta sa Sanata Muhammad Danjuma Goje ya zauna da shugaban jam’iyyar APC na kasa da kuma wasu daga cikin ‘yan majalisarsa a jiya.

Bayan haka, an yi irin wannan taro tsakanin Ministar hakokin mata, Pauline Tallen wanda ta hakura da neman takarar Sanatar kudancin jihar Filato a APC.

Shi ma Sanatan kudancin Kebbi, Bala Ibn Na’alla ya hadu da Adamu a kan yadda za a bullowa zabe.

Zamfara babu baraka

Ku na da labari cewa bayan shekaru kusan hudu ana ta rigimar cikin gida, duka Gwamnonin Zamfara daga 1999 zuwa yau sun dawo sheka daya a tafiyar APC.

Sabon shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu ya yi namijin kokari wajen sasanta Gwamna Bello Matawalle da bangaren Abdulaziz Yari da tsagin Kabiru Marafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel