Sakamakon umarnin da aka bada, mai ba Buhari shawara ya ajiye aiki domin neman Gwamna

Sakamakon umarnin da aka bada, mai ba Buhari shawara ya ajiye aiki domin neman Gwamna

  • Ita Enang ya rubuta takardar murabus da ta tabbatar da ya ajiye aikinsa a fadar shugaban Najeriya
  • Sanata Ita Enang ya godewa Muhammadu Buhari da ya yi aiki da shi na tsawon shekaru kusan 7
  • Hakan na zuwa ne bayan Muhammadu Buhari ya bukaci duk masu neman takara su ajiye aikinsu

Abuja - Ita Enang ya yi murabus a matsayin babban mai taimakawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da nufin yin takarar gwamna a 2023.

Tribune ta kawo rahoto a ranar Litinin da ya tabbatar da cewa Hadimin ya aika da takardar murabus zuwa ga fadar shugaban kasa a farkon makon nan.

A takardar da ya rubuta, Enang ya godewa Mai girma shugaban kasa da ya ba shi damar aiki a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

Sanata Ita Enang wanda ya kasance mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin Neja-Delta zai nemi kujerar gwamnan jihar Akwa Ibom a jam’iyyar APC.

Enang ya ce dalilinsa na ajiye aiki shi ne neman tsayawa takarar gwamna a jam’iyya mai mulki. A cewarsa, ya yanki fam, yana neman tutar APC mai mulki.

Murabus din Ita Enang

“Lokacin ya zo. Ina da niyyar neman takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyarmu ta APC.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai ba Buhari shawara
Sanata Ita Enang Hoto: pmexpressng.com
Asali: UGC

“Jam’iyyar da na ke so ta tsaida ni a matsayin ‘dan takara bayan na saye fam, kuma na cike takardun zabe.”
“Saboda haka ina mai gabatar da takardar murabus dina daga ofis, domin harin zama gwamnan jiha.”

Enang ya godewa Buhari

“A watan Agustan 2015, Mai girma shugaban kasa ka nada ni a matsayin mai bada shawara kan harkar majalisa.”

Kara karanta wannan

Matashi ‘Dan shekara 38 ya fito zai jarraba sa'a a takarar Shugaban kasa a zaben 2023

“Na yi kokarin wannan aiki wanda ya zarce kowane irin hidima tsakanin masu zartarwa da majalisa wahala a tarihi.”
“Na zarce wa’adin farko, aka fara wa’adi na biyu, mu ka yi aiki da jam’iyya wajen zaben shugabannin majalisa.”
“Bayan nan ka sake nada ni a matsayin babban mai bada shawara a harkokin Neja-Delta daga Agustan 2019 zuwa yau.”

- Ita Enang

Ko da ya sauka daga kan wannan kujera, an rahoto tsohon Sanatan ya ce a shirya yake ya bada gudumuwarsa ga gwamnatin Muhammadu Buhari da jam’iyya.

Tarihin siyasar Ita Enang

Ku na da labari Ita Enang ya taba wakiltar mutanen Itu da Ibiono na jihar Akwa Ibom a majalisar wakilan tarayya na tsawon shekaru 12 tun daga 1999 zuwa 2011.

A shekarar 2011 ne Enang ya yi nasarar zama Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas a majalisar dattawa, bayan zaben 2015 ne ya bar majalisa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel