Magana biyu: Bayan sun nuna su na goyon bayan Tinubu, ‘Ya ‘yan APC sun ce su na tare da Amaechi

Magana biyu: Bayan sun nuna su na goyon bayan Tinubu, ‘Ya ‘yan APC sun ce su na tare da Amaechi

  • Masu tsaida dan takara a jam’iyyar APC a jihar Kaduna sun yi alkawarin zaben Rotimi Amaechi
  • ‘Ya ‘yan jam’iyyar sun ce za su ba Amaechi kuri’unsu duk da kwanaki sun fadawa Bola Tinubu irin haka
  • Nasir El-Rufai ya wanke kan shi daga baki biyun da ‘yan APC suka yi, ya ce shi kuri’a daya gare shi

Kaduna - Masu zaben ‘dan takara a jam’iyyar APC daga jihar Kaduna, sun nuna za su goyi bayan Rotimi Amaechi ya zama ‘dan takarar shugaban Najeriya.

The Cable ta ce Rotimi Amaechi ya ziyarci Kaduna, inda ya gana da ‘yan jam’iyyar APC wadanda suka nuna masa za su mara masa baya a zaben tsaida gwani.

Ministan sufurin kasar ya hadu da ‘ya ‘yan APC na reshen jihar ne a ranar Lahadin nan da ta wuce.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Da yake jawabi a wajen taron, Mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yabi Amaechi. Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan ya karbi Bola Tinubu.

Nasir El-Rufai ya ce masu tsaida gwani sun yi na’am da Tinubu ba tare da sauraron sauran wadanda ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ba.

“Na fada maku a lokacin da ku ka yi wa Asiwaju alkawari, watakila saura ba za su zo ba, a dalilin abin da ku ka yi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amaechi
Rotimi Amaechi a Kaduna Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook
“Kun yi zabi ba tare da kun saurari sauran (masu neman takara ba). A yau kun ga bambancin da ke tsakaninsu.”
“Kun saurari Rotimi Amaechi, kun ga abubuwan da ya yi. Sannan ya zo dauke da tawaga mai cike da tsaro.”
“Saboda haka kun san abin da zai faru game da sha’anin tsaronmu idan ya karbi ragama.”

Kara karanta wannan

Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

- Nasir El-Rufai

'Dan Amana zai samu kuri'a?

Jaridar ta ce El-Rufai ya sake jaddada cewa akwai bukatar shugabancin Najeriya ya koma hannun mutumin kudu saboda a samu adalci da daidaito a 2023.

Gwamna El-Rufai ya tambayi ‘yan jam’iyyar ko su na tare da ‘Dan Amanar Daura, kuma suka amsa cewa su na tare da shi a matsayin ‘dan takaransu a APC.

Bayan nan sai aka ji Gwamnan yana cewa ya yi tunanin za su marawa Tinubu baya ne, har ya zarge su da yin baki biyu, ya ce zai yi duk abin da suka ce masa.

Inda matsalar Buhari ta ke - Bala

A ranar Lahadi aka ji Sanata Bala Mohammed ya ce wasu mayaudara da makaryata suka zagaye shugaba Muhammadu Buhari, shi kuma bai fahimci hakan ba.

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce Katsinawa irinsu Umaru ‘Yaradua sun kawo cigaba a Najeriya, amma Muhammadu Buhari ya gaza gyara kasar nan.

Kara karanta wannan

Saraki ya bada labarin zamansa Shugaban Majalisa a 2015 duk da adawar Bola Tinubu a APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng