Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

  • Olubankole Wellington ko kuma Banky W kamar yadda aka fi saninsa ya shigo jam’iyyar PDP
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi wa mawakin maraba ta musamman
  • Tauraron ya sauya-sheka daga Modern Democratic Party da nufin zama ‘dan majalisa a 2023

Lagos - Mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Dr. Bukola Saraki, shi ne wanda ya yi wa Olubankole Wellington maraba a PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci a ranar Talata, 10 ga watan Mayu 2022, tsohon shugaban majalisar dattawan ya karbi fitaccen mawakin a jam’iyyar PDP.

Dr. Bukola Saraki ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya tabbatar da cewa ya hadu da Banky W, har ya kuma yi masa lale maraba da shigowa cikinsu.

“Na yi farin cikin yi wa Banky W maraba zuwa #officialPDPNig tare da Jandor!”

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

- Bukola Saraki

Maganar da Saraki ya yi a Twitter da karfe 4:22 na yammacin jiya na cigaba da jawo martani daga masu amfani da kafofin sada zumuntan na zamani.

Mawakin Najeriya, Banky W
Bukola Saraki tare da Olubankole Wellington (Banky W) Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Abin da ake fada a Twitter

“Ana ta cika jam’iyyar PDP ta reshen jihar Legas da matasa masu basira. Idan suka hada-kai, za su samu nasara tare.”

- Baba Tee

PDP Vanguard ta yabi ‘dan takarar, ta ce:

"Mai neman kujerar shugaban kasan da ya fi kowa aiki, cigaba da hada-kan jam’iyyarmu."

...Ba za su kai labari ba

Akin Adejola ya ce PDP ba za ta ci zabe ba:

"Dukkansu za su sha kashi ne. Maganar gaskiya, abin da ya sa Legas ta ke cigaba shi ne tun 1999, PDP ba ta taba yin mulki ba. Duk jihohin da (PDP) suka yi mulki, sai an samu ci baya. Shiyasa ake tururuwan zuwa Legas domin a dace."

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

"Ni ba ‘dan a-mutun siyasa ba ne, amma a matsayina na ‘dan siyasa a jihar Legas, na san shigarsa PDP ba dabara mai kyau ba ce. Amma ina girmama zabin da ya yi, kuma ina yi masa fatan alheri."

- Great Bulala

Banky W ya bar MDP

Jaridar Daily Post ta ce a watan jiya Olubankole Wellington ya bada sanarwar dawowa jam’iyyar PDP da nufin takarar kujerar ‘dan majalisar tarayya.

Wellington yana harin zama ‘dan majalisar wakilan yankin Eti-Osa a majalisar tarayya a zabe mai zuwa, yana sa ran samun tikiti, ya gwabza da APC.

Hakan na zuwa ne bayan wannan mawaki ya yi watsi da jam’iyyar hamayya ta Modern Democratic Party wanda ta ba shi damar takara a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel