Shirin 2023: Atiku na neman kuri'u, ya bayyana manyan manufofinsa guda biyar kwarara

Shirin 2023: Atiku na neman kuri'u, ya bayyana manyan manufofinsa guda biyar kwarara

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana wasu manufofi guda biyar da yake yiwa kasar tanadi
  • Dan siyasar wanda yake neman darewa kujerar Buhari ya lissafa manufofin nasa na son hada kan kasar, magance matsalar rashin tsaro, tattalin arziki, ilimi, da sake fasalin kasa
  • Ya kuma jadadda cewa ba za a cimma wannan manufar ba har sai sun hada kansu a matsayinsu na 'ya'yan jam'iyyar PDP

Abia - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a ranar Lahadi, ya ce yana da wasu manufofin ci gaba guda biyar da ya tanadarwa kasar idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Atiku wanda ya gana da wakilan PDP na jihar Abia a babban taron jam’iyyar na kasa a dakin taro na gidan gwamnati, ya lissafa manufofinsa na ci gaba guda biyar da suka hada da; hada kai, magance matsalar rashin tsaro, tattalin arziki, ilimi, da sake fasalin kasa, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Shirin 2023: Atiku na neman kuri'u, ya bayyana manyan manufofinsa guda biyar kwarara
Shirin 2023: Atiku na neman kuri'u, ya bayyana manyan manufofinsa guda biyar kwarara Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa kudu maso yamma shi ne ainihin inda ya sa a gaba, yana mai cewa:

“Don haka, ba wanda zai iya kirana da sunan mai adawa da yankin gabas ko mai nuna wariya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta rahoto inda yake cewa zuwa 2023, PDP za ta cika shekaru 8 a matsayin mai adawa, yana mai cewa:

“Ya zama dole mu lashe zabe na gaba. Shin za mu so komawa? Shin za mu so ci gaba da kasancewa cikin adawa? Wadannan sune tambayoyin da ke gabanmu.”
“Burinku a matsayin ‘yan kabilar Igbo zai tabbata. Don haka ku ba ni nasara domin burinku ya tabbata.
“A tare za mu iya cimma wadannan manufofin idan muka hada kai a matsayin PDP sannan mu kwato mulki.”

Ya kara da cewa:

“Na zo da wadannan manufofin kuma idan kuka bani wannan dama, ina ganin za mu yi aiki tare don cimma hakan.”

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

'Dan takarar PDP ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara gyara Najeriya yadda ake sa rai

A wani labarin, ‘Dan takarar shugaban Najeriya kuma gwamnan Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed yana ganin Muhammadu Buhari bai fahimci siyasa ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu 2022, da ya nuna cewa Bala Abdulqadir Mohammed ya kai ziyara zuwa jihar Katsina.

Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya ziyarci jihar shugaban kasar ne da nufin samun goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a zaben fitar da 'dan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel