2023: Kwankwaso ne zai zama shugaban Najeriya, inji jigon siyasa Buba Galadima
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya shiga tsaren takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam'iyyar NNPP mai tasowa
- Wani tsohon mamba a kwamitin amintattu (BoT) na APC, Buba Galadima, ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kano ne kadai ya sayi fom din tsayawa takarar jam’iyyar NNPP
- Gabanin zaben 2023, Galadima ya lura cewa fitowar sabuwar jam'iyyar na baiwa sauran jam'iyyun siyasa ciwon kai a Najeriya
Buba Galadima, wanda tsohon mamba ne a kwamitin amintattu na jam’iyyar APC mai mulki, ya ce Rabi’u Kwankwaso shi ne dan takarar jam’iyyar NNPP ba tare da dan hamayya ba.
Galadima ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano ne kadai ya sayi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, inji rahoton The Cable.
Galadima wanda da dan tsagin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kara da cewa daukakar jam’iyyar NNPP na sanya sauran jam’iyyun siyasa kwanan-zauna.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Jam’iyyu biyu kawai ake da su a Najeriya a yau: NNPP da sauransu. Ita ce jam'iyya mai nasara.
“Shekararta 22 amma an sake farfado da ita watanni biyu da suka wuce. Mun ga kashin bayan duk wadanda kuke tsoro saboda sun san cewa dan takararmu ne zai zama shugaban Najeriya na gaba, da yardar Allah.”
Da aka tambaye shi sunan dan takarar, sai Galadima ya ce:
“Muna da fom dinmu, mun rufe siyar da fom. Mutum daya ne ya siya fom don zama shugaban kasa, don haka ba shi da abokin hamayya.
“Shine dan takara daya tilo a Najeriya wanda ya tabbatar da cewar zai kasance kan takardar zaben a watan Maris 2023.
“Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance dan siyasa daya tilo a Najeriya wanda ya mallaki takardun da babu wanda ke da shi a tsakanin dukkanin masu takara a fadin kasar.
“Ya kasance mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya kasance sanatan tarayyar Najeriya, ya kasance ministan tsaro, ya kasance jakada mai cikakken iko. Ya yi gwamnan jihar Kano na shekaru takwas.
“Babu dan Najeriya a yau da ke da wadannan cancantar da kwarewar.”
Ikirarin Buba Galadima ya yi karo na kalaman Boniface Aniebonam
Wannan ikirari na Galadima ya yi karo da kalaman Boniface Aniebonam, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa na farko.
Da farko Aniebonam ya bayyana cewa yan takara uku ne suka nuna kudirinsu na son mallakar tikitin shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar.
A wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), Aniebonam ya ce yan takara uku ne suka nuna aniyar neman takarar kujerar a jam’iyyar.
Rikicin siyasar Kano: A yau Shekarau zai fice daga APC, zai hade da Kwankwaso
A wani labarin, mun ji cewa a yau ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zai bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki.
Shekarau, wanda ke jagorantar bangaren G-7 na APC a Kano, ya samu sabani da Gwamna Ganduje, duk da cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a makon da ya wuce ya kawo karshen kungiyar G-7, inda a karshe aka mika ragamar shugabancin jam’iyyar ga tsagin gwamnan.
Wasu jiga-jigan APC da dama sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng