2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

  • Yayin da ake ci gaba da jiran zaben 2023, 'yan takarar APC sun ce za su bar jam'iyyar saboda wata manakisa da ke cikinta
  • 'Yan takarar a jihar Filato sun bayyana hakan ne bayan gano wata makarkashiya a da hanyar zaban dan takara
  • Ya zuwa yanzu dai jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen zabukan fidda gwani gabanin 2023

Filato - Dukkanin yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Filato sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar idan ba a bi tsarin da ya dace ba wajen zabar wanda zai rike tutar ta ba.

Shugaban kungiyar yan takarar gwamnan APC, Cif Amos Gizo, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a taron manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Sanin hannu: Dan takarar shugaban kasa a APC ya raba kafa, ya sayi fom din sanata

Gizo, wanda ya kasance dan takarar gwamna, ya bayyana cewa duk wani yunkuri na Gwamna Simon Lalong na tursasa dan takara kan jam’iyyar da mutanen Filato zai fuskanci turjiya.

Yadda siyasar APC jihar Filato ta sauya salo, 'yan takara za asu sauya sheka
2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Mambobin kungiyar sun hada da mataimakin gwamnan, Farfesa Sonni Tyoden; Farfesa Dakas Dakas, Sunday Biggs da Dr. Patrick Dakum. Ya bayyana cewa jawabin yarjejeniya da matsayin yan takarar gwamna na APC 18 ne a jihar.

Ya kara da cewa dukkansu suna da kishin aikin Filato, “dukkan mu muna da sha’awar canza labarin zuwa sabuwar Filato mai tsaro da ci gaba.”

A cewarsa, a taron farko na kungiyar da aka yi a watan Afrilun 2022, duk masu son tsayawa takara sun yanke shawarar cewa bai kamata a tursasa kowane dan takara ba, inda ya kara da cewa, ko da za a fitar da dan takarar maslaha zai kasance a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

Sun kuma yarda cewa gaba dayansu za su goyi bayan duk dan takara da ya zama na maslaha.

Ya ce:

“Wannan taron manema labarai ya zama dole saboda abun da yake kamar jita-jita na shirin tabbata da yanayin da gwmanan jihar, Lalong ke abubuwa.
“Duk mun yarda cewa wannan aiki na bi ta kan dimokradiyya ya samu amincewar gwamna, don kawai a yi watsi da zabin jama’a da kuma tursasa dan takarar da bai yi suna ba wanda zai jawo wa jam’iyyar illa a matsayin dan takarar da suka fi so."

Ya ce dukkan yan takarar sun yanke shawarar gabatar wa jam’iyyar dan takarar maslaha, wanda zai iya doke sauran ‘yan takarar jam’iyyar.

Almajirai da Fulani sun sha alwashin kawowa Jonathan kuri'u 14m

A wani labarin, wata kungiyar arewacin Najeriya da ta hada da Fulani makiyaya da al'ummar Almajirai, a ranar Litinin a Abuja ta ce ta shirya bai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan kuri'u miliyan 14 a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

Kugiyoyin sun sanar da cewa sun siyar da shanunsu masu yawa domin tattara N100 miliyan na siyan masa fom din takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Idan za a tuna, a ranar Juma'a, 22 ga watan Afirilun 2022, wata kungiya ta tsinkayi ofishin tsohon shugaban kasan da ke Abuja inda ta bukace sa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel