Karin bayani: Tinubu ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fidda gwani na APC

Karin bayani: Tinubu ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fidda gwani na APC

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matakin da zai dauka idan ya ga sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai zuwa
  • Shugaban na APC ya shaida wa mabiyansa cewa su kwantar da hankalinsu domin ya yi mafi yawan ayyukan da ake bukata domin ya samu nasara
  • Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya ce idan ya fadi a zaben fidda gwani, zai amince da shan kaye ne ya koma gida ya huta

Najeriya - Asiwaju Bola Tinubu, daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki ya magantu kan abin da zai yi idan ya fadi a zaben fidda gwani da jam'iyyar ta shirya yi.

Bayanan na Tinubu na zuwa ne jim kadan bayan da rahotanni suka yadu kan cike ka'ida da ya yi kana da mayar da fom din takarar APC ga shugabannin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Dan takarar shugaban kasa ya magantu
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fidda gwani na APC | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Depositphotos

Ya kuma tabbatar wa mabiyansa cewa zai yi nasara. Sai dai ya ce idan ya sha kashi, zai amince da shan kaye ba tare da wani kurnu ba.

Tsohon gwamnan jihar Legas a cikin bidiyon ya fadi cikin harshen Yarbanci cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan suka kayar da ni, zan koma gida."

A cewar wata sanarwa dauke faifan bidiyo da Jubril A. Gawat ya yada a Twitter, ya bayyana irin kokarin da Tinubu ya yi kana da yadda ya yi imani da da duk abin da ka iya biyo baya.

Gawat ya fassara kalaman Tinubu da cewa:

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce a shirye yake ya yi zaben fidda gwani kuma duk abin da ya faru, zai dauka sai dai ya tabbatar wa dimbin magoya bayansa a fadin kasar nan cewa ya yi mafi yawan ayyuka kuma kowa ya sa ransa a inuwa."

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama

'Ya'yan APC dai na ci gaba da zuba ido ga zaben fidda gwanin 'yan takara, inda duk wanda ya sayi fom zai san matsayarsa.

Kalli bidiyon:

Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

A wani labarin, jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya mayar da cikakken fom dinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyarsu ta APC a yau dinnan.

Tinubu ya mika fom din ga ofishin jam’iyyar ne a ranar Laraba 11 ga watan Mayu a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu, da dai sauransu ne suka wakilci Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel