Saraki: Na Kayar Da Tinubu a Lokacin Da Na Zama Shugaban Majalisar Dattawa
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya kai wa wakilan jam’iyyar PDP ziyara a Jihar Legas inda ya bukaci su mara masa baya don ya tsaya takara a jam’iyya
- Ya sanar da su yadda ya kayar da wanda ya lashi takobin ba zai zama shugaban majalisar dattawa ba, inda ya yi masa warwas sannan ya dare kujerar
- Idan ba a manta ba, a lokacin Saraki yana APC a zaben 2015 ya yi takara da wanda babban dan takarar da jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mara wa baya
Legas - Dan takarar shugaban kasa kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Sarki, ya samu damar ganawa da wakilan jam’iyyar PDP a Legas, inda ya roke su akan su mara masa baya don ya tsaya takarar shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.
Ya sanar da wakilan cewa shi ne dai nasu wanda ya kara da babban da takarar da ake ji da shi wanda ya lashi takobin ba zai ci nasarar zama shugaban majalisar dattawa kuma ya samu nasarar.
Idan ba a manta ba, Saraki a lokacin yana jam’iyyar APC ya zama shugaban majalisar dattawa a 2015 wanda su ka kara da wanda babban dan takarar jam’iyyar APC da ake ji da shi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mara wa baya.
Saraki ya ce har kokarin cire shi daga shugaban majalisar dattawa an yi amma abin ya ci tura
Yayin da ya ke jawabi a taron kamar yadda Daily Trust ta nuna, Saraki ya ce ya kayar da babban dan takara, wanda tsohon gwamnan jihar kuma mai son tsayawa takarar shugaban kasa ya mara wa baya. Ya ce zai taimaka wa jam’iyyar wurin dawo da karfinta jihar a 2023.
A cewarsa, saboda kokarin sulhun da ake ta yi, an samu hadin kai a Legas da sauran jihohi kamar Filato, Ogun da Oyo.
Saraki ya ce an kasa cire shi a matsayin shugaban majalisar dattawan saboda abokan aikinsa su na matukar sonsa.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng