Keƙe da ƙeƙe: Bayan janye takara, Adamu Garba ya fidda sunayen wadanda suka tara masa N83.2m

Keƙe da ƙeƙe: Bayan janye takara, Adamu Garba ya fidda sunayen wadanda suka tara masa N83.2m

  • Bayan karaya da kuma janyewa daga takarar gaje Buhari, Adamu Garba II ya fito ya yi bayani game da kudin da aka tara masa
  • Adamu yace zuwa yanzu an tara masa kudi sama da miliyan 80, kuma yana shirye ya mayarwa jama'a kudaden
  • Ya kuma godewa masoyansa tare da fada musu hanyar da za su bi wajen karbar kudin da suka tura masa cikin sauki

Najeriya - An wayi gari da samun labari mai daukar hankali, inda Adamu Garba, dan takarar shugaban kasa a APC ya bayyana ficewarsa daga jerin 'yan takara tare da barin jam'iyyar.

Bayan bayyana dalilansa na ficewa daga APC da kuma janye takarar, jim kadan Adamu ya fidda wani jerin sunaye dauke da wani banki da cewa su suka tara masa gudunmawar takara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

Idan baku manta ba, tun farko Adamu ya nemi masoyansa a Najeriya su tara masa kudin sayen fom din takara na APC, wanda aka sanya masa farashin N100m.

Batun kudin takarar Adamu Garba II
Keke da keke: Bayan janye takara, Adamu Garba ya fidda sunayen wadanda suka tara masa N83.2m | Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Bayan shafe kwanaki ana tara masa kudaden ne sai kwatsam labari ya karade kafafen sada zumunta cewa ya ma janye gaba daya daga takarar, kuma zai yi bayani daga baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakilin Legit.ng Hausa ta bi shafin Twitter na Adamu Garba II, inda ya ga jerin sunayen da ya saki tare da yin bayani game da ci gaban.

Duk da cewa rubutun basu fita da kyau ba, alamu na nuna takardun banki ne tare da jerin shigar kudi cikin asusun bankin daga ranar da aka fara tura masa kudin zuwa lokacin da ya sawwaka.

A bangare guda, Adamu ya shaidawa masoyansa zai mayar musu da kudadensu idan suka bukata tare da yi musu godiya da nuna soyayya da kwarin gwiwa akansa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

A sabon rubutun da ya yi dauke da hoton sunayen, Adamu ya ce:

“Kamar yadda muka yi alkawari, ga cikakken jerin wadanda suka bayar da gudunmawar yakin neman zabenmu ta yanar gizo, ga masu bukatar a mayar musu da kudin, to ku nuna sunan ku, ku aiko da shaidar biyan kudin da ta dace, za mu duba, mu tabbatar sannan mu mayar da kudin inshaa Allahu. Allah ya albarkace ku, ya kuma albarkaci Najeriya."

Ga sunayen kamar haka:

Wakilin Legit.ng Hausa ya gana da wani dan-a-mutun Adamu Garba II, Haruna Musa, wanda ya bayyana ra'ayinsa kan sauya dabarar dan takarar da yake so.

Ya shaida mana cewa, bai da matsala da sauya shekar, kana shi yana cikin wadanda suka tura kudi, kuma ba zai karbi nasa ba saboda burinsa yaga matashi ya mulki Najeriya ne a kowace jam'iyyar.

Ya ce:

"Adamu Garba dai ban taba haduwa dashi ba, amma nakan bi harkokinsa ta Twitter da Facebook, kuma na gamsu da manufofinsa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

"Shawari ne mai kyau yadda ya bar APC, saboda jam'iyyar ta nuna mahandama za ta bai wa tikti don haka zai bata lokaci ne kawai a cikinta. Shi yasa naji dadi da ganin ya bar APC kuma na kara jin ina kaunar tafiyarsa.
"Maganar mayar mana da kudi, ba zan nemi a biya ni ba tunda dama na bashi ne saboda ya cimma burinmu mu matasan Najeriya. Kuma ina da kwarin gwiwar zai yi abin kirki idan Allah ya bashi dama."

Bayan An Tara Masa N83m Don Siyan Fom Ɗin Takara, Adamu Garba Ya Fice Daga APC, Ya Bayyana Dalili

A wani labarin, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Adamu Garba ya sanar da murabus din sa daga jam'iyyar mai mulki a kasa.

Garba, wanda ya fice daga takarar shugaban kasa bayan masu gudunmawa sun tara masa N83m, ya soki jam'iyyar kan tsadan kudin fom din wato N100m.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ya ce hakan wani yunkuri ne na yi wa matasa da sauran yan takara masu nagarta kora da hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel