Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

  • Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki wani yankin jihar Kaduna, sun hallaka mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 20
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun kai farmaki ne cikin dare, inda suka kwashe wasu mutane
  • An ce sun tafi da yara da mata tare da wasu masu rike da sarautun gargajiya a yankin Chikun na jihar ta Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kurmin Sata da ke da tazarar kilomita kadan daga Millennium City a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu akalla 20 a yankin.

A cewar daya daga cikin shugabannin JTF na yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 12:16 na daren Asabar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da Limamin masallacin Juma'a

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 20 a Kaduna
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 20 a Kaduna | Hoto: thenationonilineng.net
Asali: UGC

A cewarsa, a cikin mutane 20 da aka yi garkuwa da su, mutane hudu sun tsere daga hannun masu garkuwar, wadanda suka mamaye al’umma da manyan makamai, Leadership ta ruwaito.

Ya bayyana cewa Hakimin kauyen da wasu masu rike da sarautar gargajiya, mata da yara na daga cikin wadanda aka sace, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A cewarsa:

"Yayin da 'yan bindigar ke ta harbe-harbe ba kakkautawa, harsashi ya kashe mutum daya a gidansa."

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da Limamin masallacin Juma'a

A wani labarin, wasu ‘yan ta’adda sun kashe akalla manoma 7 da babban limamin masallacin Juma’a na garin Faru mai suna Malam Sani Akwala a ranar Asabar, a kauyen Dajin Danau da ke kauyen Faru a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

An birne Deborah, dalibar da aka kashe kan batanci ga Manzon Allah (SAW)

An kai harin ne da misalin karfe 12:45 na rana lokacin da 'yan ta'adda kusan 30 dauke da makamai suka kai farmaki a gonakin da ke Faru, wanda ke da nisan kasa da kilomita daya.

‘Yan ta'addan sun hadu da manoman ne a lokacin da suke aikin sassabe a gonakinsu. Da ganinsu, sai wasu manoman suka gudu domin tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel