Namadi wanda ya yi wa Jonathan mataimaki, ya fadi wanda ya fi dacewa da takara a PDP
- Abubakar Bukola Saraki ya yi zama da shugabannin PDP na Kaduna domin tallata masu kan shi
- A wajen zaman, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Muhammad Namadi Sambo ya yabi Saraki
- Namadi Sambo ya kawo dalilan da ya sa yake ganin ya kamata PDP ta ba Saraki tikitin zaben 2023
Kaduna -Tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Muhammad Namadi Sambo ya ce Dr. Abubakar Bukola Saraki zai dace da rike shugabancin kasa.
Jaridar Leadership a wani rahoto da ta fitar a ranar Talata, ta ce Arc. Muhammad Namadi Sambo ya bayyana hakan ne da Bukola Saraki ya ziyarci Kaduna.
Abubakar Bukola Saraki ya yi wani zama na neman iri tare da jagorori da ‘ya ‘yan PDP na reshen jihar Kaduna da nufin samun kuri’a a zaben tsaida gwani.
Da yake jawabi, tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaida cewa shi da Saraki sun yi gwamna tare tsakanin 2007 da 2011, kuma ya san shi da kishin Arewa.
'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya
A cewar Namadi Sambo, tun a wancan lokaci da Saraki yake rike da mulki a jihar Kwara, ya kan damu da halin da Kaduna da Arewa maso yamma ke ciki.
“Zan tuna a lokacin da na ke kan kujerar gwamna, ya ba jihar Kaduna kula ta musamman."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sambo ya ji dadin aiki da Bukola Saraki
“Da yake kujerar shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, wasu lokutan sai in rika ji na kamar mataimakinsa"
“An samu wannan ne saboda yadda mu ka yi aiki tare da kuma alaka mai kusancin da ke tsakaninmu."
“Ina so duk ku sani cewa Saraki mutum ne mai tafiya da mutane. Mutum ne mai yi da kowa, mai yi domin su.”
Saraki ya yi aiki a Kwara da Majalisa
Legit.ng ta ce Sambo ya cigaba da yabawa tsohon gwamnan na jihar Kwara, ya ce a lokacin da yake shugaban NGF, ya kawowa duka jihohin PDP cigaba.
A game da harkar gona, jigon na PDP ya ce gwamnatin Saraki ta bunkasa noma a jihar Kwara, har aka kafa gonakin Shonga wanda a yau kowa yake koyi da su.
A karshe Sambo ya ce ganin nasarorin da Saraki ya samu a majalisa, zai yi kyau a tsaida shi a PDP.
Jonathan zai yi takara?
A ranar Litinin da yamma aka ji labari Goodluck Ebele Jonathan ya sa labule da shugaban APC, Abdullahi Adamu, aka yi wani zama a gidansa a garin Abuja.
Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan ganawa da shugaban APC ne jim kadan bayan an saya masa fam din takara. A karshe Jonathan bai karbi wannan fam ba.
Asali: Legit.ng