2023: Duk da ya ki karbar fam din da aka saya masa, Jonathan ya hadu da Shugaban APC

2023: Duk da ya ki karbar fam din da aka saya masa, Jonathan ya hadu da Shugaban APC

  • A ranar Litinin da yamma ne Goodluck Ebele Jonathan ya sa labule da Sanata Abdullahi Adamu
  • Dr. Goodluck Jonathan ya yi zama na musamman da Shugaban APC a gidansa da ke garin Abuja
  • Tattaunawar ta biyo bayan wasu sun biya N100m, sun saye fam din takara da sunan tsohon shugaban

Abuja - Yayin da ake cigaba da jin jita-jita su na yawo a kan takarar Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar ya hadu da shugaban jam’iyyar APC na kasa.

A daren Talatar nan, jaridar Vanguard ta rahoto cewa Dr. Goodluck Jonathan ya yi zama na musamman da shugaban APC watau Sanata Abdullahi Adamu.

Manyan sun tattauna ne a game da batun takarar da ake rade-radin Goodluck Jonathan zai yi a APC.

Rahoton ya ce Jonathan wanda ya yi mulki a karkashin jam’iyyar PDP ya hadu da Sanata Adamu ne a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

An yi wannan zama ne bayan labule, ba tare da an san abin da ya wakana tsakanin ‘yan siyasar ba. Amma ana zargin ba zai wuce batun takarar shugaban kasa ba.

Majiyar ta ce Jonathan ya hadu da shugaban jam’iyyar ta APC ne da kimanin karfe 9:00 zuwa 10:00. Bayan nan ba iya samun jin ta-bakin wani a cikinsu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jonathan ya hadu da Shugaban APC
Goodluck Ebele Jonathan da Sanata Abdullahi Adamu Hoto: @Theresa Tekenah
Asali: Twitter

Yadda aka shawo kan Jonathan

Wata majiya ta shaida cewa ko da Jonathan ya nuna ya yi watsi da tayin takara da aka yi masa bayan an saya masa fam, a baya ya yi tunanin jarraba sa’arsa.

Har zuwa ranar Asabar, tsohon shugaban Najeriyan ya yi niyyar shiga takara a APC, amma wasu manyan na kusa da shi, su ka ba shi shawarar ka da ya bar PDP.

Wadanda suke zagaye da Jonathan sun nuna masa ko da ba zai shiga harkokin jam’iyyar adawar ba, bai kamata a ga tsohon shugaban kasa ya sauya-sheka ba.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Abin da makusanta suka nunawa Jonathan shi ne, zai bata sunansa a idanunan Duniya muddin ya karbi tayin takarar shugaban kasa a makare a APC mai mulki.

A dalilin hakan ne ake zargin tsohon shugaban kasar ya yi zama da Adamu na kusan sa’a guda a Abuja, inda kowanensu ya fahimci juna a karshen tattaunawar.

An sayawa GEJ fam

A jiya ne aka samu rahoto wata kungiyar Dulani ta sayawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan fam domin ya nemi takarar shugaban kasa a APC.

Kwanaki an ji wasu mutane sun yi tattaki zuwa ofishin tsohon shugaban kasar, su na ta huro masa wuta a kan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel