Daga karshe: Bayan kus-kus da dare, an gano dalilin ganawar shugaban APC da Jonathan
- A daren ranar Litinin ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu
- Wannan ganawa dai ta janyo cece-kuce a siyasar kasarnan, kasancewar ganawar Jonathan da Adamu ta zo ‘yan sa’o’i kadan bayan da wata kungiyar Arewa ta siya masa fom din takarar shugaban kasa a APC
- Sai dai, a wani lamari na baya-bayan nan, an bankado ainihin dalilin da ya sa tsohon shugaban kasar ya gana da jigo a jam’iyyar APC
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a daren ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, abin da ke tabbatar da abin jita-jita game da sauya shekar Jonathan zuwa jam’iyya mai mulki.
Ganawar ta ranar Litinin ta zo ne sa’o’i uku bayan da wata kungiyar Fulani makiyaya ta biya Naira miliyan 100 domin karbar fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ga Jonathan.
A cewar jaridar Leadership, ainihin dalilin da ya sa jiga-jigan biyu suka gana shi ne don tattaunawa kan muradin Jonathan na komawa shugabancin kasar nan a 2023.
A halin da ake ciki, wannan ne karo na farko da Jonathan ya gana da shugaban kowace jam’iyya tun bayan da ya bar mulki a shekarar 2015.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake jawabi jim kadan gabanin siyan fom din a dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja, shugaban kungiyar ta Fulani, Ibrahim Abdullahi, ya ce Jonathan ne shugaban kasa mafi karamci na farko tun bayan samun ‘yancin kai a Najeriya.
Ikirarin da majiyarmu ta yi
A cewar kafar yada labaran, majiyoyin da ke kusa a lokacin taron na Litinin sun ce dukkan jiga-jigan biyu, wadanda gwamnoni ne tsakanin 2003 da 2007, sun tattauna muradin tsohon shugaban na komawa shugabancin Najeriya a 2023.
Majiyar kusa da jiga-jigan ta ce:
“Kun san Sanata Abdullahi Adamu da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gwamnonin Nasarawa da Bayelsa ne a tsakanin 2003 zuwa 2007. Dukkansu suna PDP. Bisa nufin Ubangiji, su biyun a yanzu suna cikin APC, Allah na abinsa ta hanyoyi masu ban mamaki."
Jonathan ya yi martani
Wani abin mamaki a lokacin da tsohon shugaban kasa Jonathan da shugaban jam’iyyar APC na kasa ke ganawa, wata sanarwa da ta fito daga ofishin gidauniyar Goodluck Jonathan ta bayyana cewa Jonathan bai tsaya takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Wasu dalilan na daban
Sai dai wasu majiyoyi sun ce mai yiwuwa an yi wannan bayani ne a matsayin martani ga dimbin tambayoyi da ‘yan jarida ke yi a kan lamarin, da kuma rashin samun damar isa ga tsohon shugaban da yake ganawa da shugaban jam’iyyarsa ta kasa.
Wata majiyar daban
Wata majiya ta bayyana wa kafar yada labarai cewa:
“Ku manta da abin da Gidauniyar Jonathan ta fada. Idan har yanzu kamar yadda za su so, shugabansu bai koma APC ba, me ya ke yi a gidan shugaban jam’iyyar APC na kasa da dare bayan ‘yan sa’o’i kadan bayan wata kungiya ta saya masa fom din takarar shugaban kasa?”
Majiyar ta tabbatar da cewa lallai tsohon shugaban kasar ya koma jam’iyyar APC ne a unguwarsa ta Otuoke da ke jihar Bayelsa
Mai magana da yawun Buhari ya tabbatar da sauya shekar Jonathan
Majiyar ta kuma ja hankali kan wani sako da aka wallafa a shafin Twitter a daren ranar Litinin, ta hannun hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad.
Mai magana da yawun Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter:
"To Goodluck Jonathan ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP, kuma yanzu ya zama mamba a babbar jam'iyyar mu ta All Progressives Congress (APC)."
Ahmad ya kara da cewa:
“Ba wanda zai bayar da Naira miliyan 100 don siyan fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar da ba mamba ba. Babban ma'auni na jam'iyyu wajen sayar maka da fom din su shine cewa dole ne ku fara zama mamba mai rijista."
Koma dai menene, duniya na zuba ido, kuma abin da ya buya zai bayyana; a juri zuwa rafi.
Ta kanmu mu ke, ba ta kashe N100m ba: Miyetti Makiyaya sun musanta sayen fom ga Jonathan
A bangare guda, kungiyar Fulani ta Miyetti-Allah MACBAN, ta ce ba ta sayi fom din tsayawa takara ga wani dan takara da zai fafata a zaben 2023 mai zuwa ba, inji rahoton Daily Nigerian.
Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin ne rahotanni suka ce kungiyar Fulani makiyaya ta sayawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, duk da cewa ya ki amincewa da hakan.
Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren kungiyar ta MACBAN na kasa, Baba Ngelzarma, a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, ya nisanta kansa da kungiyar ga wannan ci gaba.
Asali: Legit.ng