2023: Abin Da Jonathan Ya Ce Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takara a APC

2023: Abin Da Jonathan Ya Ce Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takara a APC

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom din takarar shugaban kasa da kungiyar fulani ta siya masa
  • Jonathan, ta bakin mashawarcinsa Ikechukwu Eze ya ce bai aike su ba kuma 'cin mutunci' ne a siya fom da sunansa ba tare da neman izininsa ba
  • Ya kara da cewa har yanzu bai yanke shawarar cewa zai amsa kirar magoya bayansa ya shiga takarar ko akasin hakan ba yana mai kira da mutane su yi watsi da siyan fom din

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom ɗin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progresives Congress, APC, da wata kungiyar magoya bayansa daga arewa suka siya masa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Jaridar The Cable ta ce Ikechukwu Eze, mashawarcin Jonathan a bangaren watsa labarai, ya bayyana hakan awanni bayan labarin cewa an siya masa fom ɗin yana mai cewa ba a nemi izinin tsohon shugaban kasar ba kuma ya dauki shi a matsayin 'cin mutunci'.

2023: Abin Da Jonathan Ya Ce Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takara a APC
Jonathan Ya Yi Watsi Da Fom Ɗin Takarar APC Da Aka Siya Masa.
Asali: Facebook

Ban aike kowa ya siya fom din takara da suna na ba - Jonathan

"Muna son mu fayyace cewa Dr Jonathan bai san da batun ba kuma bai bada izini ba," wani sashi na sanarwar ta ce.
"Muna son mu bayyana cewa idan tsohon shugaban kasar na son takara zai bayyana niyyarsa ƙarara ga al'umma kuma ba zai shiga ta bayan gida ba."

A baya-bayan nan dai an yi ta kira da Jonathan ya shiga takarar shugaban kasar amma ya umurci magoya bayansa su jira.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Zan fito fili karara in sanar da takara ta idan na yi shawarar yin hakan - Dr Jonathan

"Duk da muna godiya bisa goyon baya da yan Najeriya da dama ke nuna masa ya fito takarar shugaban kasa a 2023, har yanzu bai riga ya amsa kirar ba," a cewar Eze.
"Siyan fom din takarar shugaban kasa da sunan Dr Jonathan ba tare da izinin sa ba, duba da matsayin da ya rike a kasan nan cin mutunci ne. Don haka ana kira ga al'umma su yi watsi da batun."

Hadakar kungiyoyin arewa ne suka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar kamar yadda suka sanar da yan jarida a Abuja.

Sanye da huluna 'face kap' dauke da rubutun 'kayi takara Jonathan, kayi takara' mambobin kungiyoyin sun ce Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa ya yi takarar shugabancin kasa bayan Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasar ya bar wa cikinsa abin da zai yi bayan watsi da tayin da aka masa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Siyan fom din shine abu na baya-baya da aka yi don janyo hankalinsa ya shiga takarar.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164