Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zaiyi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zaiyi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

  • Alamu sun fara tabbatar da cewa tsohon shugaban ƙasa Jonathan ba zai yi takarar shugaban ƙasa karkashin APC ba a 2023
  • Wata majiya ta ce babu wasu alamun Jonathan ya cike Fom ɗin da aka saya masa, kuma a ranar Jumu'a APC zata kulle karba
  • Wata kungiyar Fulani a arewa ce ta jagoranci saya wa Jonathan Fom ɗin tsayawa takara karkashin jam'iyya mai mulki

Abuja - Alamu sun nuna cewa da yuwuwar tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, ba zai nemi takarar shugaban kasa ƙarƙashin APC ba.

Vanguard ta gano cewa Fom din APC na miliyan N100m da kungiyar Fulani ta saya wa Jonathan a makon nan, har yau ba'a cike shi ba bare a maida wa jam'iyya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Goodluck Jonathan.
Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A yau Jumu'a, 13 ga watan Mayu, 2022 jam'iyyar APC ta tsara rufe karɓan Fom daga hannun yan takara bayan sun kammala cike wa.

Wata majiya da tsakar ranar Jumu'an nan ta shaida wa jaridar cewa:

"Tsohon shugaban ƙasan na duba abubuwa da dama kuma ba zamu iya cewa ya cike Fom ɗin takara da aka siya masa ba ko kuma ba zamu iya cewa yana da sha'awar neman takara a APC ba."

Hakan ya biyo bayan furucin shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Bayelsa, wanda ya tabbatar da cewa Jonathan bai zama cikakken mamba a APC ba.

Sai dai ya ce kofar su a buɗe take, a shirye jam'iyyar APC take ta karɓi tsohon shugaban da duk wanda ke da sha'awar shigowa cikin inuwarta.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Tuni dai wata ƙungiyar Fulani a arewa ta lale miliyan N100m.ta karɓi Fom din takara da sunan Jonathan, lamarin da ya ce ba'a tuntuɓe shi ba.

A wani labarin kuma Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Kallo ya koma sama baki ya ƙi rufuwa yayin da Sanata Kwankwaso ya dira Kano daga Abuja tare da jiga-jigan APC mai mulki.

Tsohon hadimin Buhari, Kawu Sumaila, Albdulmumini Jibrin, suna cikin tawagar da ta dira Filin Malam Aminu Kano tare da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel