Yanzu-Yanzu: Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC

  • Wata kungiyar fulani ta siya wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa a inuwar APC
  • Kungiyoyi da dama sun dade suna kira ga Goodluck Jonathan ya fito takarar shugabancin kasar a 2023 amma ya ce a saurare shi
  • A halin yanzu dai ba a riga an ji daga bakin tsohon shugaban kasar ko zai yi takarar ba kuma ko zai shiga jam'iyyar ta APC mai mulkin kasa

Abuja - A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke cigaba da karatowa, wata kungiya karkashin 'kungiyar fulani' ta siya wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa kan N100m, Vanguard ta rahoto.

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa
Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC. Hoto: TVC News.
Asali: Twitter

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa
Kungiyar Fulani Ta Siya Wa Gooduck Jonathan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa. Hoto: TVC News.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Hotunan da TVC News ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna wasu cikin shugabannin kungiyar dauke da fom ɗin.

Matasa sun yi tattaki zuwa ofishin Jonathan sun bukaci ya fito takara

Idan za a iya tunawa a watan Afrilu 2022, wasu mutane sun yi tattaki zuwa ofishin tsohon shugaban kasa Jonathan, suna bukatar ya fito ya yi takarar shugaban kasa a 2023.

Mai magana da yawun kungiyar, Mayor Samuel, wanda shine jagoran 'Youth Compatriots of Nigeria' ya ce:

"Wasu da suka ce mana za su iya yin aikin a shekarar 2015 sun yaudare mu.
"Yanzu mun gane gskiya, karkashin mulkin Jonathan, albashi mafi karanci zai iya siya maka buhun shinkafa. Yanzu me muke da shi a yau? Muna rokon tsohon shugaban kasa Jonathan ya yafe mana, mun gane kurenmu, muna so ya dawo ya karasa abin da ya fara."

A martaninsa, Jonathan ya ce na san kun 'zo ne domin ku nemi in fito takara, ba zan iya fitowa ba a yanzu domin har yanzu akwai wasu abubuwa da ke tafiya.

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

"Kuna kira in fito a zabe mai zuwa. Ba zan iya cewa zan fito takara ba. Ana tuntuba, ku jira ku gani. Muhimmin abin da za ku yi shine ku nemi wani da zai yi aiki tare da matasa."

A yau, karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, da gwamnan Cross Rivers Ben Ayade sun siya fom din takarar shugaban kasa a Abuja.

Saura da suka siya fom din na APC sun hada da ministan sufuri Rotimi Ameachi, Gwamna Kogi Yahaya Bello da sauransu.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel