Shirin 2023: Gwamnan CBN ya tafi kotu neman damar tsayawa takarar gaje Buhari
- Gwmanan CBNya tafi kotu domin kalubalantar yunkurin AGF da INEC na hana shi tsayawa takara har sai ya sauka daga mukaminsa
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan yada labarin yiwuwar fitowar gwamnan na CBN takara a zaben shugaban kasa na 2023
- Bayanan da ya shigar gaban kotun sun bayyana bukatarsa, inda yace shi ma'akacin gwamnati ne ba dan siyasa ba
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa, inda ya kawo karshen kame-kame kan yunkurinsa na tsayawa takara, The Nation ta ruwaito.
A karar da ya shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja ta hannun Cif Mike Ozekhome (SAN), yana neman a bayyana cewa ba zai yi murabus ba domin ya shiga fafuukar takara har zuwa zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.
Gwamnan babban bankin na CBN ne kadai ya shigar da karar, inda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ke a matsayin wadanda ake kara.
Yana rokon kotu ta tabbatar da ko sashe na 84(12) na dokar zabe ta 2022 bai sabawa sashe na 137 (1) (G) na kundin tsarin mulkin 1999 ba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Wani bangare na dalilan bukatar ya yi bayanin cewa:
“Wanda ya shigar da karar na da burin neman zabe a ofishin Shugaban Tarayyar Najeriya da kuma shiga jerin 'yan takara a zaben 2023 mai zuwa.
“Cewa sashe na 84 (12) na dokar zabe, 2022 ya tanadi cewa: ‘Babu wani dan siyasa a kowane mataki da zai zama wakili mai kada kuri’a ko a zabe shi a babban taro ko taron gangamin kowace jam’iyyar siyasa domin gabatar da ‘yan takara na kowane zabe'.
“Cewa wanda ya shigar da kara ya yi imanin cewa wadannan tanade-tanaden ba su shafe shi ba, domin shi ba dan siyasa ba ne kamar yadda tanadin sashe na 84 (12) na dokar zabe, 2022 ya tanada.
"Cewa Babban Bankin Najeriya gaba daya (100%) mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya ne, don haka ya zama hukumar gwamnati mai zaman kanta kamar yadda sashe na 318 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada."
Atiku Abubakar: Ni nake da gogewa da kwarewar iya dakile matsalar tsaro a Najeriya
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a PDP, Abubakar Atiku, ya roki wakilai da jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Osun da su mara masa baya domin cimma manufarsa ta siyasa.
Atiku ya kuma bayyana musu irin gogewar da yake da ita, inda yace shi ne zai iya kawar da matsalolin da kasar nan ke fuskanta, musamman na tsaro.
Hakazalika, ya ce yana da gogewar da ta dace wajen hada kan Najeriya da kawo sauyin fasali mai dorewa.
Asali: Legit.ng