Rikicin Benue: Majalissar Dattawa ta fara yiwa Gwamna Samuel Ortom bincike akan kashe-kashen da ake zargin makiyaya sunyi a jihar sa
- Kwamitin bincike na majalissar dattawa ta yiwa gwamnan jihar Benue tambayoyi akan rikicin makiyaya da manoma a ranar Laraba
- IGP Ibrahim Ibrahim Idris yace akwai sa hannun gwamnan jihar Benue a rikicin da ya addabi jihar sa
Gwamna Samuel Ortom ,ya yiwa majalissar Dattawa bayyani akan kashe-kashen da ake zargin makiyaya sun yi a jihar Benue .
Kwamitin dake kula da al’amuran ‘yansanda da jami’an lekan asiri ta yiwa gwamnan bincike a ranar Laraba 14 ga watan Fabrairu.
Kwamitin suna masa bincike ne akan zargin da Sfeto Janar ‘yansadan Najeriya, Ibrahim Idris, yayi masa na cewa, da sa hanun a rikicn da ya addabi jihar sa.
KU KARANTA : Ku daina yada tsoro da janyo tashin hankali a kafofin watsa labaru – Gwamnatin tarayya
Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin da shugaban ‘yasandan Najeriya yace sanya dokar hana kiwo a fili da gwamna, SamueL Ortom, ya zartar a jihar Benuwe ya janyo rikicin makiyaya da manoma a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng